GYARAN JIKI

Ma'asumah Nigeria News Update.

M.N.N.U.030

Da farko dai shi gyaran jiki yana matukar bukatar kulawa tare kuma da daukan lokaci. musamman idan akace jikin is very dry. amma hausawa sukace hakuri da dauriya shi ke kai mutum ga samun nasara. duk da cewa a farko zaki ga kamar baya aiki amma duk inda kika dauki wata daya, wata biyu, kina yi dole sai an ga chanji a tare da ke. akwai hanyoyin gyaran jiki kamar haka

1-RUWA

Kamar yanda nasha fada shan ruwa da yawa yafi komai muhimmanci ga rayuwan dan adam. rashin ruwa a jiki yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare da wuri. rashin ruwa a jiki yana sa saurin tsufa da saurin kamuwa da cututtuka masu dama. dan haka muke shawartan mutane da su rika shan ruwa akalla kofi takwas zuwa goma a ko wacce rana. sannan ruwan ya kasance tsaftatacce.

2-WANKA

Yin wanka sau biyu a rana na daya daga cikin manya manyan hanyoyin gyaran jiki

• Tsaftataccen ruwa, soso mai laushi, sannan a yayin zaben sabulun wanka mutum ya nemi na kalar fatar sa wato dry skin oily, normal skin ko kuma for all skin types.

3- TAUSHIN FATA ( EXFOLIATE )
Yin wannan sau biyu zuwa uku a sati yana kankare dattin jiki tare da kankare matattun cells din dake saman fatan mutum wanda hakan ke haifar da taushi tare da santsin fata. Zaki same shi a shagon kayan kwalliya dauke da suna kamar haka EXFOLIATING CREAM KO BODY SCRUB sannan zaki iya hadawa a cikin gida kamar haka:-

GA MASU YAWAN MAIKO A JIKI KO FUSKA

• Lemun tsami
• Suga ko gishiri
• Ki kwaba ruwan lemun tsami da suga kafin sugan ya gama narkewa ki riqa deba gina goge fuskan dashi.
• bayan minti 30 ki dauraye da ruwan sanyi. Sau daya zuwa biyu a sati

GA MASU YAWAN BUSHEWAN JIKI

Suga ko gishiri gwangwani daya

Man zaitun ko almond ko man cika gida (castor oil) rabin gwangwani.

Zuma kwatan gwangwani.

• Lavenda oil ko wani mai kamshi chokali daya.

• Ki hada su wuri daya bayan kin gama wanka ki shafa shi ki dan dirje jikin ki dashi sannan ki jira minti biyar ki dauraye da ruwa ki fito.

• Wannan hadin zai kai tsawon sati biyu ba tare da ya lalace ba.

GA WADANDA JIKINSU bashi da wata matsala, za su iya amfani da kowanne daga cikin wadannan biyun.

4-YAWAITA SHAFA MAI
Mutane da yawa basa son shafa mai ajikin su suna ganin cewa ba wata damuwa to akwai damuwa kokuma a shafa a kafa da hannu da fuska kadai shi yasa lokuta da dama sai kaga jikin mutum yayi dabbare dabbare ko ina kalarsa daban. Please mu riqa amfani da man shafawa masu kyau bana bleeching ba. Idan kinyi amfani da wannan baki ji dadin sa ba kar ki kuma sayan irinsa ki nemi wani har sai kin samu wanda kika ji dadin sa daga nan sai ki cigaba da siyan irinsa. Sannan ya kamata mu san wannan:-

• BODY CREAM KO BODY LOTION wannan a jiki kadai ake shafawa banda fuska shafa shi a fuska zai iya kawo matsala kamar na kunan rana, kuraje, da sauran su.

• FACE AND BODY CREAM\LOTION wannan zaki iya amfani dashi a jiki da kuma fuska baki daya.

• FACE\FACIAL CREAM wannan fuska kadai.

• Da sauran su. Al’muhim dai, mutum ya karanta rubutun bayanin da ke jikin mai sosai sannan ya duba kwanan watan da man zai lalace wato expiring date kafin ya saya.

5-KARE JIKI DAGA RANA

Rashin shiga rana yana daga cikin abinda yasa jikin yara yake da taushi da sheqi. Don haka duk lokacin da mutum zai fita ya riqa yawan amfani da sun protecting cream (SPF). Musamman ga mata masu amfani da man bleachin rana zai iya kona fuskar ta zama ja idan basa neman kariya daga rana.

Bugu Da Kari:

SANTSI DA SHEKIN FATA

• Aloe vera gel chokali daya.

• Kurkum rabin karamin chokali.

• Zuma chokali daya.

• Madara chokali daya.

Ki kwaba su gaba daya ki shafa daga fuska zuwa wuyan kin a tsawon minti 20-30 ki wanke da ruwan dumi.

NA BIYU ZAKI SAMU
• Gwanda ko kabewa dan kadan
• Garin sandal karamin chokali.

• Zuma chokali daya.

Ki kwaba sosai ki shafa na tsawon minti 20-30 ki wanke da ruwan sanyi.

NA UKU ZAKI SAMU
• Ruwan rose (rose water).

• Bayan kinyi wanka da safe da daddare ki rika shafa shi yana bushewa ajikin ki kafin ki shafa mai

YANDA AKE HADA ROSE WATER.

• Zaki samu fulawan rose ki tsitsigeta ta kai kaman kwatan kofi sannan ki sa ruwa sama sama ki dauraye ta, ki dauko tafasashen ruwan ki da ya huce rabin kofi ki tace ki zuba a roba mai tsafta, sannan ki zuba furen acikin ruwan ki rufe ki lullube shi ckin kaya mai duhu na tsawon kwana uku ki juye a tukunya mai tsafta ki dafa har sai kinga kalar furen ya bace sannan ki sauke ki tace ruwan. Ki bari yayi sanyi sannan ki fara amfani dashi. Wannan hadin zai kai tsawon wata daya baiyi komai ba matukar an hada shi da ruwa mai kyau. A gaba zamuyi bayani akan amfanin rose water inshaa Allah.

GYARAN HANNU DA KAFA

TAUSHIN HANNU.

Ki nemi hand cream mai kyau ko kuma

• ki nemi man kwakwa ki ajiye a kusa duk lokacin da kika gama wani akin gida ki dauraye hannun ki ki shafa, da daddare ma haka kafin ki kwanta.

• Ki nemi man zaitun ki kwaba da suga ko gishiri ki riqa goge hannunki da shi sannan ki shafa mai ki sa safan hannu ki fara aikin ki.

TAUSHIN KAFA.

• Ruwan dumi kisa man kwakwa kadan a ciki ki tsoma kafarki bayan ruwan ya huce sai tsame kafar ki sa dutsen goge kafa sama sama kid an goge fatar da suka taso sannan ki dauraye ki goge da tawul ki shafa man kade ki kulle da leda ki sa safa (musamman ga masu kaushin kafa).

• Yawaita shafa wa kafar mai har tafi zai taimaka wurin lausasa ta.

Ma'asumah Nigeria News Update

Tare daGYARAN JIKI.

Tare da Sakina Ahmad da Khadija Muhammad 

Post a Comment

Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post