Kwamishnar kiwon lafiyan jihar, Dakta Tomi Coker, wacce ta bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da manema labarai a Abekuta, babbar birnin jihar, ta ce ya fara zazzabi ne kuma aka fara jinyarsa a asibitin dake cikin kamfanin Lafarge kafin komawarsa Legas ranar Laraba.
Kwamishanar, tare da kakakin gwamnan jihar, Remmy Hazzan, da manyan ma'aikatan ma'aikatar sunce masana kwayoyin cuta sun fara tattara dukkan wadanda ya hadu da su a lokacin da je jihar.
Kwamishanar ta ce mutumin ya hadu mutane uku kafin zuwansa jihar Ogun ranar Talata.
Tace: "A awanni 12 da suka gabata, an gano bullar cutar COVID – 19 (Coronavirus) a Najeriya kuma mutumin da ke dauke da cutar ya ziyarci jihar Ogun."
"Mutumin dan kasar Italiya ne, ma'aikaci ne a kamfanin Lafarge dake Ewekoro. Ya zo Najeriya ranar 24 ga Febrairu misalin karfe 9 na dare."
Kafin isarsa jihar Ogun, ya gana da mutane uku, ya kwana a Legas kuma ya zo Ogun da safiyar Talata."
Darakta Janar na Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria, Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Abuja.
Ihekweazu yace wajibi ne asibitoci su lura sosai su zauna cikin shiri.
Tags:
Labaran Duniya