@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YAQIN KHAIBAR YA QARA FITO DA FALALAR IMAM ALI (A.S)
Duk wata falala ta gaskiya da za ka samu ta wani Sahabi, to, Imam Ali (A.S)yana da ita da kuma qarin wasu falalar wadanda shi kadai ya kebanta da su.
Wannan kuma ba yana nuna cewa Sahabbai ba su da falala bane, a'a, sai dai kawai a nuna mana ne cewa shi Imam Ali (A.S)ya fifita ne a kansu kamar yadda Annabi (S.A.W.W)ya fifita kan sauran Annabawa da Manzanni (A.S).
Ibn Asakiri ya fitar daga Ibn Abbas (R.A)yace,
‘’ DUK WANI ABINDA AKA SAUKAR KAN WANI (na falala ko yabo)CIKIN LITTAFIN ALLAH YA SAUKA AKAN ALIYU (R.A).‘’
Yaqin Khaibar yaqi ne wanda ake kira (SARIYYA), wato,wanda Annabi (S.A.W.W)ya tura Sahabbansa bai yi tarayya da su a cikinsa ba.
Yaqi ne wanda Annabi (S.A.W.W)ya tura Abubakar ya jagoranci runduna don yaqar mutanen Khaibara, da ya gagara sai aka tura Umar Bn Khaddab. Shima ya dawo ba tare da nasara ba, wannan dalili yasa aka tura Imam Ali (A.S).
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Sahal Bn Sa'ad da ma waninsu cewa, Annabi (S.A.W.W)yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ GOBE ZAN BADA TUTA GA WANI MUTUM, KUMA ALLAH ZAI YI BUDI A HANNUNSA. YANA SON ALLAH DA MANZONSA, KUMA SHIMA ALLAH DA MANZONSA NA SONSA .‘’
Sai mutane suka wayi gari kowa na so ya ji ance shine. Da gari ya waye sai suka tafi wajen Annabi (S.A.W.W), kowa na buqatar ace shine. Sai Annabi (S.A.W.W)yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ INA ALIYU BN ABIY 'DALIB ?‘’
Sai aka ce, yaa ma'aikin Allah, ai ba shi da lafiya. Sai yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KU AIKA AZO MIN DA SHI !‘’
Sai yayi masa tofi a idon nasa ya kuma yi masa addu'ah, sai ya warke tamkar ma bai yi wani ciwon ido ba. Sannan ya ba shi Tuta.
Sai Aliyu yace;‘’ NA YAQE SU HAR SAI SUN KASANCE KAMAR MU (masu sallamawa)?‘’
Annabi (S.A.W.W)yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ JE KA AKAN SHA'ANINKA, HAR SAI KA SAUKA AKAN FARFAJIYARSU SANNAN KA KIRAYE SU ZUWA MUSLINCI, KUMA KA BA SU LABARIN ABINDA YA ZAMA WAJIBI A KANSU. WALLAHI, DA MUTUM 'DAYA (1)ZAI SHIRYU TA DALILINKA YA FI ALKHAIRI GARE KA FIYE DA A BA KA GARKEN JAJAYEN RAQUMA !‘’
Imam Ali (A.S)ya tafi, kuma Allah ya bada nasara ta hannunsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~17th March, 2020.