Tsohon Jami’in CIA: An Kirkiro Cutar Coronavirus Ne Don Cimma Wata Manufa Ta Kiyayya
kwararre kana kuma tsohon jami’in ƙungiyar leƙen asirin Amurka CIA ya bayyana cewar cutar nan ta Coronavirus ba haka kawai ta bayyana ba, face dai an ƙirƙiro ta ne a ɗakin gwaje-gwaje, wataƙila da nufin amfani da ita don yaƙar wanda ake so a yaƙa.
Philip Giraldi ya bayyana hakan ne cikin wata maƙala da aka buga a jiya Alhamis ya ce akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa akwai wasu ɓangarori na ƙwayar cutar ta Corona da ba haka kawai suka bayyana ba, alamu na nuna cewa an ƙirƙire su don cimma wata manufa ta yaƙi.
Tsohon jami’in CIA ɗin ya ƙara da cewa: Akwai wasu bayanai da suke nuni da cewa sakamakon yadda gwamnatin Amurka ta Trump take ci gaba da nuna damuwarta dangane da irin ci gaban da China take samu wanda Amurkan take ganinsa a matsayin barazana ga tsaron ƙasarta, don haka akwai yiyuwar Amurkan ce ta ƙirƙiri ƙwayar cutar da nufin dunƙufar da China a ɓangaren tattalin arziki da ayyukan soji.
Mr. Giraldi ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko da hakan take faruwa ba, yana mai cewa a shekarar 2005 zuwa 2009, Amurka da Isra’ila a asirce sun ƙirƙiro wani virus na kwamfuta mai suna Stuxnet da nufin cutar da na’urorin kwamfutar da Iran take amfani da su wajen shirin nukiliyanta na zaman lafiya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake irin wannan zargi na yiyuwar an ƙirƙiro ita wannan cutar ta Coronavirus wacce ya zuwa yanzu ta kama mutane sama da 90,000 tun bayan ɓullarta a ƙasar Chinan a watan Disambar bara sannan kuma ta kashe mutane sama da 3000 ya zuwa yanzu.