FARIN JININ SHUGABA BUHARI KAFIN 2015 DA BAYAN YA SHEKARA BIYAR AKAN KARAGAR MULKI.


 ✍️ MUSA IBRAHIM  DAURA

Na kasance daya daga cikin masoya buhari, tun bansan inda yake min ciwo ajiki na ba, domin tun Alif da Dari dara da tamanin da biyar,(1985) lokacin da akayi masa juyin mulki nakeson buhari shekara talatin da biyar baya kenan, har yanzu kuma ban daina ba, saidai inajin takaici da ciwon yadda lamura ke tafiya musamman a wannan mulki nasa na farar hula.
SHUGABA BUHARI 


Kamar yadda na kasance masoyinsa akwai miliyoyin mutane a fadin kasar nan da suke so da kaunar Buhari kamar su hadiye shi, basu son suji ana muzantashi ko yakar sa, daidai da kwayar zarra! saidai suma a yanzu basu jin dadin yadda abubuwa ke wanzuwa a karkashin wannan mulki nasa.

Ina da tabbacin cewa ba'a taba samun wani shugaba ba, musamman Dan adawa a kaf fadin najeriya Wanda yayi farin jini tare da samun karbuwa kamar shugaba buhari, birni da kauye, yara da manya, maza da mata, kowa sai BUHARI SAI BABA, SAI MAI GASKIYA. Mai karatu zai yarda dani akan cewa ba komai ya jawowa buhari wannan farin jini da karbuwa ba, ila Abu biyu zuwa uku. Na farko shine;-

1.Gaskiya
2.Rikon Amana
3.kishin kasa da al'umma.

Wadannan halaye sun bayyana tun yana yaro har zuwa shugabancin sa na kasa da rikon PTF, mutane sunga yadda buhari ya yaki cin hanci tare da yaki da rashin gaskiya a lokacin mulkin sa na soja, ba sani ba sabo, haka kuma anga yadda ya gudanar da aiyukan raya kasa a lokacin shugabancinsa na PTF, wadannan dalailai su suka ba jama'a karfin gwiwar tsayawa tsayin daka kancewa sai ya shugabanci kasar nan, talakkawa sunyi uwa sunyi makarbiya wajan ganin hakan ta tabbata, buhari baya da ko sisin kwabon dayake ciwo kuma baya bada ko anini amma ake tururuwar son sa.

Kafin yazama shugaban kasar farar hula, saida yazama samun Wanda ZAI KALUBALANCI BUHARI A BAINAR JAMA'A WAHALA NE, BUHARI YA ZAMA KAMAR UBA GA KOWA BA MAI IYA FADAMASA MAGANA, KO MASU ADAWA DASHI TSORON SUKAR SA SUKEYI, KAI SAIDA TAKAI TA KAWO IDAN ANASO ACI ZABE SAI AN JINGINA DA BUHARI.idan kuma mutum na adawa da buhari zaiyi wuya yaci zabe. Saboda so da kauna mutane har kati suka rika saye Wanda akayi na musamman suna turawa shugaba buhari a matsayin kudin kamfe, daga naira Dari zuwa dubu Dari, mai saida goro, ko mai tura baro ko Dan dako zaizo yace a tura masa kati zuwa ga baba Buhari, Duk anayin hakane da tunanin samun saukin rayuwa.

A Wancan lokacin idan akace ana so a nemo masu adawa da buhari abin ya zama wahala, bare Wanda zai fadawa buhari magana marar dadi baka iya samun masu sukar sa cikin sauki, kowa shakka yake, domin mutum yana iya shiga babban hadari akan sukar buhari, haka aka taho har Allah yayi nasa ikon a 2015 Allah ya tabbatarwa da buhari shugabancin kasar nan.

DUSASHEWAR FARIN JININ BUHARI SHEKARA BIYAR BAYAN YA ZAMA SHUGABAN KASA.

Cin zaben shugaba buhari ke da wuya baki dayan kasar nan aka rude da murna tare da kade kade Raye Raye, bushe bushe da wake wake, har da yanke yanken dabbobi domin nuna godiya ga Allah, mutane suka shiga murna da tunanin sauki yazo musu, buhari zai saita kasa, za'a koma bin doka da oda, tattalin arziki zai inganta, ilimi, lafiya tsaro zai inganta, aikinyi zai zama ya wadata, satar kudin gwamnati dayin facaka zasuyi matukar raguwa, fifita dangi da yan uwa tare da abokai a cikin gwamanti zaiyi karanci.

Shugaba buhari yayita sukar gwamnatocin baya akan rashin iya shugabanci, da rashin gaskiya, yayi suka akan TALLAFIN MAN FETUR  INDA YAKE CEWA DA TURANCI(WHO IS SUBSIDIES WHO?) WAI WAYAKE TALLAFAWA WANI? YANA NUFIN BABU WANI TALLAFI. shugaba buhari ya kalubalanci karin kudin fetur, inda har zanga zanga aka shiga dashi domin Karin kudin fetur, Shugaba buhari ya kalubanci yan siyasa suna azurta Kansu da yan uwansu.

Amma abin mamaki Buhari na hawa bajimawa ya kara kudin fetur, ba jimawa yaci gaba da bada tallafin kudin fetur, wani abin takaicin shine yadda wasu ke azurta Kansu da kudin gwamnati a mulkin buhari anaji ana gani, cin hanci da rashawa bata canza Zane ba, ga ciwo bashi daga kasashen waje. Kai duk wani nau'i na matsin rayuwa an shigo dashi a wannan gwamnati maimakon a samu saukin rayuwar da akayi zato yanzu sai bakar azaba ake sha kuma babu alamun ranar fita. ANYA KUWA BUHARIN DA MUKA SANI NE KE MULKIN KASAR NAN??

SHIN WAI BUHARI YASAN HALIN DA TALAKKA KE CIKI KUWA?

Tun da shugaba buhari ya hau mulki talakka ke bashi uzuri akan tunanin cewa anyi barna ne a baya, yanzu gyara akeyi jama'a sunyi uzuri, sunyi uzuri, babu abin da bai kusan limka kudinsa ba a wannan gwamnati, gaya kuma albashi na nan bai canza ba, tattalin arziki ya ruguje, kasuwanni sun zama wajan hira da barci, masu kananan jari sun cinye kudadensu, aikin leburanci baya samuwa. wahala sai karuwa take, kuma abin bakin ciki tun mutane na sa ran samun sauki har sun fara yanke kauna akan cewa sauki na zuwa, saboda basuga alamar an hau hanya ba. Duk abin da gwamnatocin baya sukeyi ayi musu zanga zanga, gwamnatin buhari tayi shi kamar Karin kudin fetur, janye tallafi, rashin Karin albashi, tashin farashin kaya, rufe kanun iyakoki, da sauran abubuwa na matsin rayuwa amma duk akayi hakuri. Saidai da alama kwalliya bazata biya kudin sabuli ba. KUMA ALAMU NA NUNAWA BAYAN WUYA SAI WATA WUYAR.

Abin da zai tabbatar maka da cewa an fara dawowa daga rakiyar wannan gwamanti shine yadda masu adawa da ita suke karuwa kullum, masu sukarta suke yawaita, masu fadamata bakaken maganganu suke kara bayyana, Masoyanta ke raguwa a kullu yaumin, yanzu ankai lokacin da idan kace kana Neman mai kare Buhari aiki ya sameka, domin mu masoyansa bamu da abin fadi Wanda zamu kare shi akan lamuran kasa, saidai muyita bundum bundum.

A magana ta gaskiya daga bakin masoyin buhari na gaskiya wato MUSA IBRAHIM DAURA, Mutane suna matukar kuka wasu na, danasani wasu har Allah ya isa sukeyi akan wannan gwamnati, domin matsin yayi matsi, kuma na tabbata makusantan buhari sun San ana matsi kuma sun San ana aibata gwamnatin buhari, talakka naji a jikinsa, wannan yana daya daga cikin abin daya taimaka akayi  ihu a Maiduguri, kuma na tabbata ba'a daina ihun ba matukar akaci gaba da tafiya haka, wallahi duk Wanda yakejin cewa gwamantin buhari tana tafiya daidai a yanzu to makiyin buhari ne,  koda kuwa shine YUSUF BUHARI, Ina fadin wannan magana ba don Ina so ba, saidai domin buhari yayi gyara ko talakkan daya zabai shi yaji dadin rayuwa  kuma yasamu abin fadi wajan  kare buhari.

SHAWARA.

Yakamata Buhari ya sani tun a nan duniya da kuma lahira babu Wanda za'a tuhuma akan wannan shugabanci nasa sai shi Buharin, Idan anyi daidai buhari idan an bata buhari, ya isa ishara babu mai zagin NAMADI SAMBO KO SUKAR ELEX EKWUEME, KO ADMIRAL IKHOMO DUK mataimakan shugabannin kasa ne, saidai kaji ana cewa GOOD LUCK KO MARIGAYI SHAGARI KO BABANGIDA SUNYI KAZA SUNYI KAZA, To kaima buhari bazata sake Zane ba. Don haka idan har kanason tsira da mutuncinka dolene ka zage damtse kasa kafar wando daya da duk wani mutum koma wanene komai kusancinka dashi matukar kaji zargi akansa kayi waje dashi daga gwamnatinka, ka nemi mutanen kirki kajawo su kusa da kai,kafin lokacin ya kure, wallahi wallahi mutane suna kuka da mulkin ka, kuma sun fara yanke kauna da samun sa'ida, don haka kafarga kafin sun farga su watse.

Abu na biyu duk wani Wanda ya zura bututun tsotsar man shanu a wannan gwamnatin yasan kansa babba da yaro mace da namiji, Idan har kunason Buhari kunaso ya tsira da girma da mutuncinsa, to kuyi kokarin gayamasa gaskiya tare da taimakamasa yadda za'a samu sauki, kuna iyaci gaba da tsotsar madarar Ku da man shanun ku tunda Allah yasa saniyar tana da nono wadatacce.

Amma a hannu daya Ku matsa ayi aikin daya dace domin samun sauki ga al'umma, wallahi mutane na fama da wahalar rayuwa matukar gaske, yanzu har an kai matsayin da babu mai jin shakkar fadawa buhari bakar magana a bainar jama'a. Maganganu masu ciwo da muni, kamar MAYAUDARI, MAKARYACI, AZZALUMI, MUNAFUKI MAI KUKAN KARYA, Da makamantan haka, wallahi abin yana bakanta mana zuciya, saidai babu yadda zamuyi.

Idan kuma Buhari da mukarrabansa sukayi biris tare dayin kememe suna zaton komai yana tafiya lafiya kamar yadda ake fada masa cewa abubuwa suna inganta, alhali ba gaskiya bane. To a karshe zaiyi danasani Ku kuma  mukarabbansa kunci amanar sa kunci ta al'umma, wallahi Allah bazai kyale Ku ba.

A takaice dai tun da buhari ya karbi shugabancin kasar nan kullum farin jininsa da kwarjininsa kara raguwa da dusashewa yakeyi, sakamakon gazawar da akayi wajan inganta rayuwar yan kasa. Ina FATAN ALLAH YASA BUHARI YA SAMU DAMAR KARANTA WANNAN MAKALA TAWA KO KUMA MAKUSANTAN SHI SU GANI SU FADAMASA TARE DA DAUKAR MATAKIN GYARA. Domin har yanzu akwai sauran lokaci, musamman Dan najeriya idan zai shekara goma yana shan wahala daya samu dadi na shekara daya sai ya mance da waccan wahalar ta shekara goma.

Allah kasa Buhari ya farga ya canza salon wannan tafiya yadda masoyansa na gaskiya zamu samu abin fadi ko bayan yabar mulki.

Musa Ibrahim Daura
1-3-2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post