Farashin Danyen Mai Ya Fadi Kasa Warwas A Duniya

(Rohoton abna.com) Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, farashin danyen man fetur yana ci gaba da faduwa a kasuwanninsa na duniya, inda farashin ganga ya kai dala 25, wanda ita ce faduwa irinta ta farko tun shekaru fiye da goma da suka gabata.
Farashin man ya fara rikitowa ne sakamakon kin yin aiki da yarjejeniyar OPEC daga bangaren Saudiyya, inda kungiyar OPEC ta bukaci rage yawan man da kasashe suke hakowa, bayan amincewar dukkanin kasashe mambobi, Saudiyya ta yi watsi da wannan batu, inda maimakon rage yawan man nata, sai ta kara yawansa.
Baya ga haka kuma bukatar danyen man ta ragu a duniya, sakamakon bullar cutar corona wadda take ta kara kamari, musamman a kasashen turai masu karfin tattalin arziki.
Baya ga haka kuma hannayen jari na duniya sun fadi kasa, sakamakon matsalolin da ake fuskanta a hada-hadar hannayen jari a halin yanzu saboda cutar corona, wanda hakan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasashen duniya.
KUBIYO TA FACEBOOK DOMIN SAMUN SAHIHAN LABARAI DA DUMI DUMINSU TA NAN KUYI LIKE NA FAGE DINMU Ma'asuma Nigerian News Updates
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post