@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
GABATARWA
Ita mace saliha abin buqata ne ga al'umma, domin ta hanyarsu ne ake samu al'umma abin alfahi.
Kasancewarta saliha ana samu ne tun daga yanayin gidan da ta taso, da kuma irin tarbiyyar da aka dorata akai daga gidansu.
Na'am, ba kowacce mace saliha bace take tasowa daga cikin gidan salihan mutane ba, domin wasu gidan za ka samu lalatattu ne amma sai su haifar da salihai, kamar dai yadda ake samun lalatattu ne cikin salihan mutane.
Allah (T)na cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YANA FITAR DA RAYAYYE DAGA MATATTU, KUMA YANA FITAR DA MATACCE DAGA RAYAYYE .‘’
(Qur'an)
To, ita mace ta gari ce take zama mata ta gari, kuma mata ta gari ce take zama uwa ta gari, sannan uwa ta gari ce take haifar da 'ya'ya na gari.
Ashe abin so ne gare ku mata ku kasance mata na gari don ku samar da 'ya'ya na gari don mayar da al'umma su zama na gari.
Insha Allahu za mu kawo wadannan dokoki cikin zubutunmu na gaba daki-daki.
Sai ku kasance da shafin Ma'asumah don samun wannan garabasa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-09039791509
~7th March, 2020.