Dokoki 17 ga mace saliha (1)




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

'Daukaka murya sama da ta maigida/miji yayin magana ta kowacce fuska ya saba doka ko koyarwar muslimci.

Duk halin da kuke ciki na sabani da mijinki bai kamata ki daukaka muryarki sama da tasa ba, domin yin haka na daga cikin rashin biyayya.

Ki kasance mai tausasa murna da kuma nuna qasqantar da kai gare shi yayin magana, cikin fushi ne ko kuma yayin nishadi.

Mijinki ya fi mahaifinki matsayi da iko a wajenki, tare da cewa hakan ba yana tauye haqqin mahaifinki ne da ke kan ki ba.

Allah (T)da kansa ya koyar da Sahabbai yadda ake yin magana da wanda ke sama da su don ya zama abin koyi ga mu na baya.

Yana fada cikin Qur'ani cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA KADA KU RIQA BAYYANA MAGANA GARE SHI (S.A.W.W)KAMAR YADDA KUKE BAYYANAR DA MAGANA TSAKANI DON KADA KU BATA AYYUKANKU ALHALI BA KU SANI BA .‘’

           (Qur'an)

To, kamar hakane, daga murya sama da ta mijinki da nufin walaqanta shi zai iya bata miki ayyukanki.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-07059911360

~8th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post