Dokoki 17 da ke kan mace saliha (9)




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Mace halitta ce mai jaraja wacce Allah ya halitta ta kuma ya karramata don fito da darajarta ga da namiji.

Sai dai kuma wasu matan ba su san wannan darajar da Allah yayi musu ba, shi yasa ba sa kiyaye wannan daraja tasu.

Wajibi ne akan mace saliha ta san cewa tana da daraja da mutunci , kuma ta kiyaye wannan mutuncin nata a wajen mijinta.

Kada ta zama tamkar marar amfani wajen mijinta sakamakon munanan dabi'unta ko rashin iya yin mu'amala mai kyau da shi ko da sauran jama'ah.

Wasu matan na zubar da mutuncinsu a wajen mazajensu, saboda haka sai ka samu mijin nata ba ya ganin mutuncinta, kuma ya riqa ganinta tamkar wani abu marar amfani wanda ba za a riqa ba shi kula ta musamman ba.

‘’ MAN SAMI'A WA FA'ALAH NAJAH ‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08126385470-09039791509

~19th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post