@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YIWA MIJI ADDU'AD IN YA RASA
Yana daga cikin dokokin (haqqi) da ya hau kan mace saliha yiwa mijinta addu'ah da qarfafarsa wajen jure rashi da tawakkali cikin halin quncin rayuwa.
Idan mijinki ya dawo gida babu komai a hannunsa na biyan buqatun gida saboda rashi, to, ki yi masa addu'ah da kuma yaba masa da qoqarin nema da yake yi, kada ki zama mai kushe masa ko ganin gazawarsa.
Nunawa miji gazawarsa zai sa sonki ya fice daga cikin zuciyarsa , amma yi masa addu'ah da nasiha zai qara sonki cikin zuciyarsa.
Maimakon mijinki ya ciyar da ku da haram gara ku mutu da yunwa ta rashin samun halal.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~15th March, 2020.