Dokoki 17 da ke kan mace saliha (7)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DOLE NE KI KULA DA MIJINKI DA KAN KANKI

Duk wani abu da za kiyi don kyautatawa wani za ki iya yin amfani da wata hanyar, misali 'ya'yanki ko wani na kusa da ke don bada kula ga wani a matsayin kyautatawa.

Kula da mijinki haqqi ne a kanki wanda ke za ki tarairaye shi da kanki kai tsaye ba tare da samar da shamaki tsakani ba.

Akwai wasu mata masu halin ko-in-kula game da mazajensu, abinda ya kamata ace su suka yi musu da kansu sai ka tarar suna sanya 'ya'yansu ne wajen aikata wannan abin.

Misali, kula da miji wajen karbar abinda ke hannunsa yayin shigowarsa gida.

Ba shi abinci ko abin sha yayin da yake buqata.

Aikata wannan da kanki shi ke nuna cewa ke uwa ce saliha mai koyar da tarbiyyar zama tare da miji ga 'ya'yanki, kuma hakan na qara sonki cikin zuciyar mijinki.

   TRIAL TO TRUST

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      07059911360

~14th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post