@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KI FIFITA SHI KAN KOWA CIKIN KOMAI NASA
Akwai wasu mata wadanda za ka iya fassara su da cewa ba su san ciwon kansu ba, ko kuma wawaye da ba su san abinda yafi musu kyau a rayuwa ba.
Irin wadannan mata sune mazajensu ba sa jin dadin zamantakewa tare da su, domin ba su cika samun abinda suke so daga gare su ba.
Sune irin matan nan da wasu ke juya akalarsu ta hanyar jansu duk inda suka so da su, kuma suka fi bin umarnin wasu fiye dana mazajen aurensu.
To, abinda ke kanki mace saliha shine ki san cewa mijinki ne ya auro ki ba wani ba, kuma shi yafi kowa iko a kanki. Saboda haka ki shagaltu da sauke dukkan wasu haqqoqi nasa da wasu qananan ayyukansa a matsayin taimakekeniyar juna.
‘’ WATA'AAWANU ALAL BIRRI WATTAQWA, .......‘’
Biyewa umarnin wasu banzayen mata ko mutane zai iya jefa ki cikin halaka matuqar suna dora ki kan sabawa mijinki wanda ya auro ki, kuma wanda ke da ikon fitar da ke.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~13th March, 2020.