Dokoki 17 da ke kan mace saliha (5)


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Abokan miji na kirki sun kasance aminai gare shi wadanda yake bude musu sirranka kuma yake neman shawarwari daga gare su don cigaban rayuwarsa da zamantakewar aurensa.

Da yawa daga cikin abokai sun fi sanin damuwar abokinsu fiye da yadda mahaifansa ke sanin damuwarsa.

Abokan miji iyaye ne ga 'ya'yanki wadanda ya kamata ku girmama su ko da kuwa bayan wafatin mijin naki ne.

Rashin girmama abokan miji yanke wani haqqi ne na iyayen 'ya'yayenki, domin daga cikin haqqoqin iyaye da ke kan 'ya'ya akwai girmama abokan mahaifa kamar yadda Annabi (S.A.W.W)ke cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ YANA DAGA CIKIN HAQQIN IYAYE AKAN 'YA'YANSU, CIKA ALQAWURAN DA SUKA 'DAUKA, SADA ZUMUNCINSU DA KUMA GIRMAMA ABOKANSU.‘’

Saboda haka kada ki munana zama da abokan mijinki don ba kya sonsu, domin wanda ya kamata ku zauna lafiya kuma ku rabu lafiya da shi shine miji. Kuma matuqar kina munana musu ba za kiyi zaman lafiya da mijinki ba.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        08126385470

~12th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post