@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
'Dabi'u ne na mafi yawan mata kwatanta mazajensu da wasu mazajen, alhali kowanne mutum akwai irin nasa matsayi wanda Allah ya ajiye shi ta hanyar neman ababen rayuwa.
Wasu mazajen suna da tsantseni wajen neman dukkan abinda za su samu na rayuwa. Su kanyi qoqarin kaucewa haram wajen abin cin su da shansu da kuma tufafinsu.
Sai dai kuma za ka tarar mafi yawan mazaje ba sa kiyaye abin cinsu da shansu wajen tantance haram da halas.
Saboda haka bai kamata gare ki yaa ke salihar mata ki kasance kina kwatantan mijinki da wasu mazajen ba, domin ba lalle ne hanyar samunsu ta zama iri daya.
Matuqar kina kwatanta shi da wasu, to, da sannu za ki ji son da kike yi masa ya soma raguwa cikin zuciyarki, idan haka ta kasance kuma za ki soma sha'awar wasu mazajen ne ba naki ba.
Kuma bai kamata ga mace ta riqa sha'awar wasu mazaje akan nata ba, ko da kuwa ya natan yake.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~11th March, 2020.