@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Allah ya halicci zuciya da bayyanar da abinda ke cikinta, wani lokaci kaga kyakkyawan abu ya fito daga gare ta, wani lokaci kuma mummuna ne ke fitowa daga cikinta.
A matsayinki na salihar mace bai kama ace ki riqa yin magana da mijinki cikin mummunan abinda ke damunki cikin zuciyarki ba.
Ko da ace akwai abinda ke damunki cikin zuciyarki, to, kada kiyi amfani ko bayyanar da shi yayin da kike magana da mijinki.
Domin gwargwadon yadda kike magana da shi gwargwadon irin fassarar da zai yi miki kenan. Saboda haka ko da wani abu ya bata miki rai kada kiyi amfani da wannan dama wajen hucewa a kansa, ko da kuwa shine ya bata miki rai.
Ba ka samun irin wannan dabi'a ga salihar mace, saboda haka sai a kiyaye.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~10th March, 2020.