@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Ita mace saliha an santa kan kyawawan dabi'u abin koyi, saboda haka cikin dokokin da ke kanta wadanda ake so ta kiyaye sun hada da;
Kada ta kasance mai bayyana gazawar mijinta a gaban 'ya'yanta ko kuma a gaban qawayenta ko da kuwa yana da gazawar.
Babu laifi ta bayyana mana ita da shi cikin girmama ba da sigar tozartawa ba, domin wasu mazajen suna nuna gazawarsu kan wani abu wanda bai fi qarfinsu ba.
Bayyanar da gazawar miji a gaban yara zai iya haifar da yaran su zo daga baya suna raina baban nasu da kuma rashin jin maganarsa, wanda a qarshe illar hakan za ta dawo kanta.
Su kuma qawayenta da ta bayyanar da gazawarsa a gaban su za su zo daga baya suna yi mata dariya da kuma ganin wawancinta a matsayin mai bayyanar da sirrin mijinta.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034-09039791509
~9th March, 2020.