Dokoki 17 da ke kan mace saliha (11)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BA A HADA SOYAYYAR MIJI DA TA WANI

Darajarta ce da mutuncinta ta kasance mai fifita soyayyar mijinta kan ta kowa.

Allah (T)ya halicci zuciya kuma ya sanya soyayya cikinta, saboda haka ba dama ace son abu guda daya(1)ke cikinta, dole a sami son wani abu na dabam cikinta.

Akwai yiwuwar ace son wani ya shiga zuciyarki kuma bai sami ikon ficewa daga cikinta ba bisa wata qaddara ko iko na Ubangiji, saboda haka abinda ya hau kanki anan shine, kada ki kuskura kina kwatanta soyayyar mijinki da ta wani dabam aboye ko a bayyane.

Ko da ace kin sami kanki cikin jarrabawa ta auren wanda ba shi kike so cikin zuciyarki ba, abinda za kiyi anan shine ki koyi sanyawa zuciyar taki son abinda ba shi take so ba, domin hakan shi yafi miki alkhairi kuma gare shi za ki sami lada ba ta hanyar son wanda Allah bai ba ki shi ba.

Jin dadin zaman gidan miji da kwanciyar hankalinki shine ki zama mai fifita son mijinki fiye da kowa.

Allah yasa mu dace.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~20th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post