CORONAVIRUS | DIREBAN WATA BATURIYA DA TA KAMU DA CUTAR A LAGOS YA TSERO GIDA KATSINA





Hukumar Lafiya Wacce Take Kula Da Cutar Coronavirus (NCDC) Taziyarci Zangon Marke Dake Jahar Katsina Karkashin Karamar Hukumar Bakori Domin Duba Wanda Ake Zargi Da Cutar COVID19...!!!

Mutumin da ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus wanda yake jahar katsina karkashin karamar hukumar Bakori bayan dawowarshi daga legos hakan yasa al ummar zangon marke suka killace shi kafinn hukumar lafiya masu kula da wannan cuta sukawo dauki.


Hakan yasamu asaline sakamokon aiki dayake karkashin wata baturiya dayake zaune a gidanta a jahar legos bayan jin ta kamu da wannan sabuwar cuta shi kuma yayi nazarin dawowa mahaifarshi zangon marke dake yankin Tsiga Bakori, a labaran da suke yawo wasu nace wa mutum da ake zargin kamuwa da cutar direban matar ne.

Hukumar lafiya ta jahar katsina karkashin jagorancin kwamishinan lafiya na jahar sun turo domin duba wanda ake zargi da kamuwa da wannan sabuwar chutar ta Coronavirus.

Hukumar lafiya wacce take kula da wannan cuta (NCDC) yanzu haka suna ta bincike akan gwajin da sukayi ma wannan mutumin wanda ake zargi da kamuwa da chutar akarshe haryanzu babu tabbacin ya kamu da cutar sai abinda sakamako yazo kowa ya zauna a gida domin kaucema wannan mummunar cuta wacce take yaduwa cikin kankanin lokaci.

Allah yakara tsare al'ummar duniya daga wannan annoba amin.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post