Darusa daga Yaqin Uhud!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

RASHIN BIN JAGORANCI KE KAWO RASHIN NASARA

Idan muka nazarci yadda yaqin Uhud ya kasance wanda yayi sanadin rasa rayukan musulmi masu yawa bai wuce rashin bin umarni ba.

Bin umarnin jagora shine babban tushe na cin nasara cikin kowacce irin tafiya, domin shine ya fi kowa sanin mafita bisa haskakawar Ubangiji.

Yawancin waqi'o'i da je faruwa mafi muni kan faru ne sakamakon rashin bin umarni ko rashin bin koyarwar jagora.

Da ace jama'ar Annabi (S.A.W.W)sun bi umarninsa a yaqin Uhud, to, da abinda ya same su bai same su ba, yaqin Badr babban misali ne.

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’,KUMA HAQIQA ALLAH TA TAIMAKE KU A BADR, ALHALI KUNA MASU RAUNI (saboda qarabcinku), KU BI ALLAH DA TAQAWA (kawai)TSAMMANINKU KUNA GODEWA .‘’

    (Al-Imran, aya ta 123)

Musulmai sunyi basara ne a Badr sakamakon bin umarnin jagora (S.A.W.W).

Wani darasi na gaba da ke cikin yaqin Uhud shine yadda aja bada kariya ga jagora. Domin a daidai lokacin da musulmai suka gudu suka bar nutane 6 tare da Annabi (S.A.W.W), su wadannan mutane 6 sai suka kasance masu bada kariya ga lafiya da kuma ran jagora (S.A.W.W).

Abu na qarshe cikin qarancin bincikena shine, an bayyanar mana da matakan imani mataki-mataki ne, gwargwadon imaninka gwargwadon dakewarka.

Saboda haka, ko da kaga dan'uwa ko 'yar'uwa na gudu a halin waqi'a kada ka zarge shi, domin Sahabbai ma sun gudu sun bar Annabi (S.A.W.W)duk da cewa ba daidai suka yi ba.

Har sai da akayi ta kiransu sannan wasu suka dawo wasu kuma suka qara yin gaba !

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE WADANDA SUKA JUYA BAYA (da gudu)RANAR DA RUNDUNA BIYU SUKA HADU, SHAIDAN NE YA SHUSSHUTAR DA SU SABODA ABINDA SUKA AIKATA (na sabawa Annabi).‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~16th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post