Dalilin komawar Imam Ali (As) hanun Manzon Allah (S.A.W.W)!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SANNU DA ZUWA YAA RENON WANDA YA FI KOWA TARBIYYAH

Allah (T)ke tsara komai nasa kuma ya hukunta shi yadda yaso ba tare da an tambaye shi ba, kuma ya ajiye baiwarsa inda yaso ga wanda yaso.

Sai dai sau da yawa akan sami sanadi na faruwar abu, walau mai kyau ko kuma mummuna.

Shi dai dalilin komawar Imam Ali (A.S)zuwa hannun Manzon Allah (S.A.W.W)shine, a shekara ta 36 bayan shekarar Giwa, wato lokacin Imam Ali (A.S) yana dan shekara shida (6), al'ummar garin Makkah sun fada cikin quncin rayuwa saboda qarancin abinci, shi kuma Abu 'Dalib (A.S)ya kasance mai yawan iyali.

Ganin haka sai Manzon Allah (S.A.W.W)ya je wajen baffansa Abbas (R.A)yace masa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ YAA BAFFANA, LALLE 'DAN'UWANKA ABU 'DALIB MUTUM NE MAI YAWAN IYALI, KUMA GA SHI ABINDA KAKE GANI YA SAMI MUTANE. MU TAFI ZUWA GIDANSA DON MU SAUQAQA MASA IYALI, KAI KA 'DAUKI MUTUM 'DAYA NI MA NA 'DAU MUTUM GUDA DON MU SAUQAQA MASA .‘’

Sai Abbas (R.A)yace, to, mu aikata mana.

Sai suka hadu da Hamza (R.A)suka tafi tare zuwa ga Abu 'Dalib (A.S) . Sai suka ce masa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE MU MUNA NUFI NE MU SAUQAQA MAKA GAME DA IYALINKA HAR WANNAN ABINDA KE TARE DA MUTANE YA YAYE .‘’

Sai yace musu, ‘’ IDAN DAI ZA KU BAR MIN 'DALIB, TO, KU AIKATA ABINDA KU KAYI NUFI .‘’

Saboda biyayya da kuma girmamawa irin ta Annabi (S.A.W.W) sai ya cewa baffannin nasa su fara dauka.

Sai Abbas ya dau Ja'afarud-'Dayyar, Hamza kuma ya dau Aqeel (R.A).

Sai Manzon Allah (S.A.W.W)yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE KUWA KUN BAR MIN ABINDA NA FI SO, MADALLAH DA WANNAN ZABI DAGA ALLAH .‘’

(Nurul-Absar, Sh:125)

Tun daga wannan rana yake gidan Manzon Allah (S.A.W.W)yasha yaci daga albarkar dake tare da shi, kuma ya kasance tare da shi cikin dukkan al'amransa har ya bar duniya.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

           09039791509

~9th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post