Kakakin sojojin ƙasar Yemen ya sanar da cewa dakarun na su tare da ɗaukin sojojin sa kai na ƙasar sun sami nasarar kwato lardin al-Jawf da ke arewacin ƙasar daga hannun sojojin hayan Saudiyya masu biyayya ga tsohon shugaban ƙasar Abd Rabbuh Mansur Hadi.
(Rohoton abna24.com) Kakakin sojojin Yemen ɗin Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yammacin jiya inda yace dakarun na su sun sami wannan nasarar ne sakamakon hare-haren da suka kaddamar kan wasu yankuna na lardin masu muhimmanci cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Kakakin sojin ya ƙara da cewa a halin yanzu dai dakarun na su suna riƙe da ikon yankunan da suka haɗa da yankunan al-Hazm, al-Maslub, al-Ghayl, al-Khalq, al-Maton and Khab wa al-Sha'af na lardin na al-Jawf yana mai cewa Saudiyya ɗin dai ta tura ɗaruruwan sojojin hayanta zuwa yankin baya ga hare-haren da ta dinga kai wa ta sama duk dai da nufin hana faɗuwar garin amma dai daga ƙarshen dakarun na su sun sami nasarar ‘yanto garin daga hannun sojojin hayar.
Har ila yau Janar Saree ya ce dakarun na su sun yi amfani da na’urorin kariya da kuma makamai masu linzami ƙirar cikin gida masu cin matsakaicin zango irin su Nikal, Qassem da kuma Badr wajen kai hare-hare inda suka sami nasarar tarwatsa cibiyoyi soji da na tattalin arziki na Saudiyyan.
Tags:
Labaran Duniya