Da Dumi-Dumi: Akwai yiwuwar karin kudin wutan Lantarki, daga 1 ga watan Afrilu



KASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Daga Bin Haroun Sigau

Ministan wutan lantarkin Najeriya Injiniya Saleh Mamman

Source: Facebook

Wani ma’aikacin kamfanin raba wutar lantarki ya shaidawa ‘Yan jarida cewa hukumar NERC ba ta aiko masu da takarda ta na neman a dakatar da karin kudin ba. Idan har abubuwa su ka tafi a haka, babu abin da zai hana daga gobe Ranar Laraba watau 1 ga Watan Afrilun 2020, jama’a su wayi gari da sabon farashin wuta.

Jaridar ta yi yunkurin tuntubar Mai magana da yawun bakin NERC, Usman Arabi domin jin matsayar hukumar game da wannan kari da ake hari a Afrilu. Arabi ya bayyana cewa ya tafi wani kwas don haka bai san maganar ba.

Jami’in da ya ke rike da wannan kujera a daidai wannan lokaci bai iya cewa uffan ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post