Kafin cutar Corona, an yi cututtuka masu yaduwa da dama wadanda suka samu tallar kafafen yada labaran duniya matuqa. Misalin cutukan su ne: Kwalara, HIV/AIDS, Ebola, LASSA, SARS, Anthrax, kai har da ma na dabbobi dangin su Bird Flu da Swine Flu. Dukkan wadannan cutuka, wadanda aka ambata da wadanda ba a ambata a nan ba, akasarinsu sun zo, kafafen labaran duniya sun yayata, jama'ar duniya ta firgita ainun, gwamnatoci kuma sun kashe maqudan kudade don rigafi ko warkar da cutukan.
A lura, manufar rubutun nan, ba don qaryata cutukan ba ne, a'a, domin fitar da wasu ababen hankalta ne wadanda marubucin nan ke fatan su qarfafi zuciyar mai karatu a wannan yanayi da ake ciki.
Cutuka masu yaduwa dai ba qarya ba ne an yi su ko akwai su. Amma abin da akasari ba su sani ba, ko kuma sun sani amma suna shakkar yiwuwarsa shi ne, bunqasar ilimi ya sa ana iya qirqirar cuta don cimma manufar samun kudi ko don cimma manufar siyasa ko duka biyun. Wadanne masu ilimi ne ke qirqirar cuta don su amfana haka? Su ne wadanda a zahiri suke amfana daga yaduwar cutar. Binciken wannan, na mai karatu ne.
A ranar 19 ga Disamba ta shekarar 2017, CNN ta wallafa rahoton wani wakilinta, Wayne Drash, mai taken: "Investigating the World's Deadliest Diseases". Faqarar farko da ta biyu na rubutun sun haskaka wannan batu na qirqirar cutar da cewa:
"The US government on Tuesday lifted a ban on making lethal viruses, saying the research is necessary to develop strategies and effective countermeasures against rapidly evolving pathogens that pose a threat to public health.
"Dr. Francis Collins, director of the National Institutes of Health, made the announcement, in which he outlined a new framework for the controversial research. The work with three viruses can now go forward, but only if a scientific review panel determines that the benefits outweigh the risks."
Ma'ana: "A ranar Talata gwamnatin Amurka ta dage dokar hana qirqirar muggan cutuka masu yaduwa, tana mai cewa, cigaba da binciken a kansu wajibi ne don zai bunqasa dabaru da hanyoyin qalubalantar sinadaran cutuka masu habbaqa wadanda suke barazana ga lafiyar jama'a.
Kafar ta CNN ta cigaba da cewa: "Dr Francis Collins, Daraktan National Institutes of Health, ya shaida haka, inda ya fitar da wani sabon tsari a kan binciken da ake taqaddama a kai. A yanzu za a cigaba da aikin samar da cutukan uku masu yaduwa, amma fa sai kwamitin masu nazarin kimiyya ya tabbatar da cewa amfanin da za a samu sakamakon cigaba da binciken ya fi hatsarin da za a fuskanta."
A cikin wannan rahoto, mai karatu zai fahimci cewa da gaske manyan gwamnatocin duniya suna qirqirar cutuka masu yaduwa. Sai dai dalilin qirqirar kuma wani turanci ne da ake son yi wa jama'a wayonsa.
A shafin YouTube, akwai wani documentary mai taken: "Engineered Viruses Are the New Biological Weapons: Here is What You Need to Know. A ciki, an nuna yadda masana kimiyya suke sanya wasu sinadarai a abinci dangin biredi wadanda suke canza hatta DNA din mutum. Haka nan an nuna yadda suke qirqiro cutukan nan masu yaduwa da ake kira "viruses" a matsayin makamai na kisa. Kazalika an nuna hoton shafin jaridar New York Times inda ta yi wani rahoto a shafinta na farko mai taken: "Scientists Create A Live Polio Virus", ma'ana: 'Masana Kimiyya Sun Qirqiro Rayayyiyar Cutar Foliyo Mai Yaduwa.'
Thabo Mbeki, tsohon shugaban Afirka ta Kudu, ya zargi Amurka da alhakin qirqirar cutar AIDS, ya ce, a dakin qera magani na sojan Amurka aka qirqiro cutar.
Ita ma mashahuriyar masaniyar ilimin dabbobi da tsirrai, 'yar qasar Kenya, Dr. Wangari Maathal, ta sheda wa duniya a filin taron lambar yabo na Nobel Peace da aka ba ta cewa:
"AIDS is not a curse from God to Africans or the Black people. It is a tool to control them designed by some evil-minded scientists."
Ma'ana: Cutar AIDS ba bala'i ce daga Allah zuwa ga 'yan Afirka ba. Dama ce ta mallakarsu, wadda wasu mugayen masana kimiyya suka qirqira."
Wakazalika Rev. Jeremiah Wright, tsohon malamin Barack Obama na addinin Kirista wanda aka sani da tsage gaskiya, ya ce, “inventing the HIV virus as a means of genocide against people of color.” Ma'ana: "An qirqiri cutar HIV ce don kisan qare dangi ga wasu mutanen da ba fararen fata ba." An ce ire-iren wadannan zantuka suka raba shi da tsohon shugaban Amurkan Barack Obama.
Zantukan wadannan mutane uku sun janyo mu su Allah-wadai daga masu fada-a-ji na duniya. Sun tashi daga matsayinsu na masu farin jini sun zama masu baqin jini domin abin da suka furta da bakinsu. Sai dai kuma abin mamaki, har zuwa yau din nan, ba a samu wani gamsasshen bayani da ya qaryata da'awar tasu ba. Kawai dai an kira abin da suka ce da qirqirarren tunani (conspiracy theory) ne. To shin, ita da'awar cewa cutar AIDS ta fara daga birrai ne a 1930 ba qirqirarren tunanin ba ne? Wane binciken kimiyya ya tabbatar da haka in banda cewa an fada da fatar baki kuma kafafen yada labaran Turai sun yayata? In kuma akwai binciken a nuna wa duniya yadda aka gudanar da shi mana.
Idan ma wannan dalilin na su Dr Wangari Maathal bai zama don rage adadin wata qabilar ba a haqiqa, abin da ya zahirta baro-baro shi ne, kamfanonin Turai sun fi kowa cin gajiyar yamadidin cutar AIDS da ake yi ta hanyar samun qazamar riba daga qera robar condom na rigafi, da qera magungunan da wai suke kira na ririta cutar ne wadanda suke sayar wa gwamnatocin qasashe masu tasowa a kan biliyoyin daloli.
Wannan shi ne misalin yadda ake qirqirar cutuka domin cimma muradai na siyasa ko na neman kudi. Cutar Corona ma na cikin wadannan cutuka. Saboda tun ba a je ko'ina ba, kafafen yada labaran Turai sun fara zabe da yada labaran siyasar durqusar da habbakan ilimin kimiyya ko tattalin arziqin qasashen da ba 'yan bangarensu ba.
Ga wasu misalai a gurguje, don na san ni da ku (masu karatu) zuwa yanzu duk mun gaji:
Daga ranar da aka ce cutar ta bulla a China, kafafen yada labaran Turai suka yi ta kai gwauro sukai mari wurin baqanta fuskar qasar. A garin da cutar ta bulla, akwai kimanin mutum miliyan 12, amma yadda aka riqa ba da labarin, kai ka ce rubu'in mutanen qasar ne ma suka mace alhali adadin wadanda suka mutun bai kai dubu uku ba har zuwa yau. China ta yi qoqari ta daqile farfagandar labaran da gina katafaren asibitin warkar da cutar a cikin mako guda tal. Amma qiri-qiri wannan bajinta bai samu yamadidin da bullar cutar ta samu ba. Daga nan ma, sai kafafen suka maida cocilar zaqular labaransu ga daidaikun mutanen da suka mutu. Suka riqa ruwaito cewa, likitocin da ke qoqarin kwantar da cutar ko warkar da ita su ma sun mutu. Kimanin mutum 20 cikinsu. Har ma da shugabansu baki daya. Wannan dabara ce ta firgitarwa, don nuna wa duniya cewa China, duk da bunqasar ilimin kimiyya da fasaharta da duniya ta shaida, ba ta da qarfin da za ta tunkari cutar.
Haka ma suke wa Iran a yanzu duk da tana ta cewa ta fara warkar da marasa lafiyan. Har ma ta ce mutanen Iraqi da suka kamu da cutar su shigo asibitocin Iran akwai magani. Amma kafafen yada labaran Turai rahoto kawai suke badawa, cewa wane ya rasu a dalilin cutar a Iran, ko an rufe masallaci saboda cutar. Sun ce Iran ce take da mafi munin labari na cutar, amma fa wadanda suka kamu da cutar mutum 139 ne. Ga kuma qasar Italiya can tana fama da wadanda suka kamu mutum 400 amma kafafen cewa suke yi Italiya na ta qorarin kwantar da fantsamar cutar. Kuma har zuwa jiya da tsakar dare, marubucin nan bai ga wata kafar yada labarai ta Turai da ta ce mutum guda a Italiya ya mutu saboda cutar ba duk kuwa da cewa mutum 400 ne suka kamu da ita, har ma gashi dayansu ya shigo da ita Nijeriya.
A kasa kunne, daga baya duniya za ta ji yadda kamfanonin maganin Amurka da Turai suka samar da wani sinadarin lafar da cutar. Sai kuma a yi ta karbar maqudan kudaden gwamnatocin da kafafen yada labarai suka firgitar a bayan sun naqasar da qima da nagartar kamfanonin qasashen da suke iya bayar da maganin cutar a arahar banza.
Tags:
Cuta da Magani