Ma'asumah Nigerian News Update
SHAFI DOMIN KAI DA AL'UMMAR KA
Daga Bin Haroun Sigau
Yunwa da talauci saiya fi yiwa talaka illah fiye da wannan cutar ta Corona Virus. A maimakon bawa talaka kariya da keɓance shi da zaman wajen guda, sai ya mutu a gida ba tare dama cutar ta kusanto ƙauyen suba.
Babban ciwon dake damun ɗan Nigeria itace; yunwa, gashi yanzun an hana masa fita neman abinci, uzuri da sada zumunci, bugu da ƙari ziyartar ƴan uwan sa da zaiyi yaji sanyi a zuciyar sa.
Karanta wannan:-A Presentation on Coronavirus Disease (Covid-19)
Tabbas, wannan cuta gaskiya ce, amma wani talaka kaji yana da ita? Duk waɗanda kaji ance sun kamu masu arziki ne, kuma wajen da suke ɗebo ta ma wani talakan ko a mafarki harya mutu bazai je ba. Ya zakuyi da waɗanda kullum sai sun fita suke samo abincin da zasu ci su da iyalin su, har suyi rayuwa cikin farin ciki??
Kuyi duba da sauran ƙasashen duniya mana, koda suka hana mutane fita kunga suna fitan?? Dalili kuwa shine basu da matsala kamar mu, ana kulawa dasu da taimaka musu. Amma nan fa? Sai business ake da wannan cuta ana ƙwamushe kudade a account din gwamanti da sunan kawo karshen wannan cuta.
Kada ku manta ance wanga cuta bata tasiri ga bakin fata da kuma waje mai zafi, gashi muna ƙasa mai zafi, a lokacin zafi, zamu ji da zafin aljihu ne kona muhallin mu?? Ba wuta, ba ruwa, ba abinci ga barazanar mutuwa koda yaushe kan wannan cuta.
Alhamdulilah, ni yadda na godewa Allah ma da duk waɗanda suke kamuwa da cutar manya ne, da yaransu, kaga dolen su zasu nemo mafita kan wannan cuta domin sunfi kowa tsoron mutuwa.
Allah Ya yaye mana wannan annoba, ya kare dukkan al'umma da irin waɗannan miyagun cututtuka. Ya Allah don girman ka da ɗaukakar ka, ka bawa Sayyid Zakzaky (H) da Malama Zeenatu lafiya, ka ƙwato mana su a hannun Azzalumai cikin izza ka ƙara musu nisan kwana.
#FreeZakzaky
#FreeUmmaZeenah
#CoronaVirus
#StaySafe
@Bin Haroun Sigau