@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SALO NE NA TATSE ARZIQIN QASA
Ba musu muke yi ba cewa wai babu wannan cuta, a'a, so muke mu tabbatarwa mutane kan cewa qirqirarta aka yi don cimma wata manufa ta Yahudawa.
Tsararren abu ne wanda Yahudu suka samar da shi don ya zama linzami na karkatar da tunanin mutane daga addininsu da kuma halin da suke ciki na quncin rayuwa.
Yana daga manufarsu hana aikata addinin muslimci da ma wasu addinai kamar kiristanci, domin su ba su da addini.
A bayyane yake idan muka kalli halin da ake ciki yanzu na hana yin wani taro da ya kai mutane 50, wanda hakan ke nuna cewa babu sallar jam'i ko yin wani taro na wa'azi.
Abu na biyu kuma shine, sun qirqiro wannan cutar ne don ta zama barazana ga arziqin qasashe, wanda a qarshe suke so su mayar da qasashe tamkar bayinsu.
Saboda haka sai suka watsa wannan cuta cikin qasashe, kuma suka kambama hatsarin da ke tattare cikinta.
KARANTA NAN:- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kama wasu motoci da suka yi yunkurin shiga Kano
Yanzu haka wannan cutar ta kasance babban makami wanda azzaluman qasa suke yin amfani da shi wajen tatsar arziqin qasa dana jihohi.
Babu batun aiki don kyautata rayuwar talajawa, dama ba yinsa ake ba. Kawai kudade ake kwasa da sunan yaqar cutar COVID-19, ana sanya su cikin asusu kuma ana tsoratar da mutane.
Talakawa na ji a jikinsu saboda quncin rayuwa, amma sakamakon wannan birgici na CORONAVIRUS ya mantar da su daga halin da suke ciki.
Su kuma azzalumai na cigaba da kwasar dukiya , talakawa na kwasar tsadar rayuwa, amma ba za su fahinci hakan ba sai lokacin da aka ce babu wannan cuta, alhali cutar ta tafi da dukiyar qasashen su.
Anan ne kuma Yahudu za suyi amfani da wannan dama su bawa qasashe bashin maqudan Dolars, sannan su shigo qasashen su mayar dasu bayi yadda basu da 'yancin kansu sai yadda su kayi dasu.
Yaa Allah ka qarawa Sayyid Zakzaky (H)kariya tare da fito mana da shi cikin izzah !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~30th March, 2020.
Tags:
Cuta da Magani