Coronavirus ko dai makircin Yahudu??? (2)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MANUFARSU SHINE HANA ADDINI DA CUTAR DA TALAKAWA

Cikin rubutunmu na baya mun fara yin addu'ah ne ga jagoran shiriya mai haskaka makircin Yahudu, wato Sayyid Zakzaky (H).

Tabbas, da yana waje da kowa ya ji haqiqanin gaskiyar wannan makirci. Suwa suka qirqirota?

Da wacce manufa aka qirqirota?

Me suke son cimmawa cikin wannan makirci?

Amma duk da cewa ba ya tare damu (MUBASHARATAN), hasken shiriyar tasa (H)na hasko mu daga gidan yari (prison).

A kwanakin baya Saudiyyah ta yi umarni hana sallar jam'i cikin masallai wanda wasu malamai yaran Yahudu suka goya musu baya cewa yin hakan na daga cikin matakan bada kariya daga yaduwar wannan cutar.

Tafiya ta yi nisa, yanzu wannan mataki nasu ya tumbatsa (burst)zuwa wasu qasashe har da wannan qasa tamu Nigeria.

Ka san wawa bai iya yin riqo da abu ba, shi in ya tashi nasa riqon sai yayi kamar zai lalatar ko halakar da abinda ya riqa.

NIGERIA TA BI SAHU

Yanzu haka wannan qasa tamu Nigeria ta bi sahu har ma ta zarci hukuncin uwar gidan tata Saudiyyah shalelen Amurka.

Cikin matakin da suka dauka su ma shine hana haduwa don yin jam'in sallar juma'ah.

Qari akan wannan shine, tsare bododi na iyakar jihohi da jihohi, babu shiga babu fita. Ma'ana babu saye babu sayarwa.

ME HAKAN ZAI HAIFAR?

Ku ce min qara jefa talakawa cikin quncin rayuwa, domin abinda ke hannunsu zai qare kuma babu hanyar shiga don sayowa daga wasu birane.

Uwa-uba kuma shine, matuqar ba a bode iyakoki ba, to, za a shiga qunci na rashin man fetur (Petrol)yayin da ya qare a gidajen mai.

An hana daidaita sahu 🧍🏻‍♂️🧍🏻‍♂️🧍🏼cikin sallah wanda malamai ke cewa sallah ba ta cika sai da daidaita sahu.

An hana yin musafaha 🤝🤝 wacce Annabi (S.A.W.W)yayi umarni da aikata, wai sai dai a riqa gaisawa daga nesa ✋🏽🖐🏼.

An hana zama cikin jama'a 👨🏼‍🦱👩🏼‍🦲👳🏼‍♀️🧕👨‍👩‍👧‍👦 wacce Annabi (S.A.W.W)yace rahma ce.

Abinda ya rage yanzu kawai shine HANA KWANCIYA DA IYALI 🥱!

Ko za ku hanu ???

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~27th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post