CORONAVIRUS | Dan kwallon kwandon Realmarid ya kamu da cutar

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bai wa dukkan 'yan wasanta umarnin killace kansu bayan da wani dan wasan kwallon kwando na kungiyar ya kamu da cutar coronavirus.

Da 'yan kwallon kafa da 'yan kwallon kwando na kungiyar na amfani da bandaki guda, wanda hakan ya sa aka dage duka wasannin Gasar La Liga tsawon mako guda.

Dama dai Tawagar kwallon kafa ta Real Madrid din za ta fafata ne da Eibar a La Liga ranar Juma'a ba tare da 'yan kallo ba.
Spaniya na da sama da mutane 2,000 da suka kamu da cutar coronavirus.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post