Iran na iya Ilimantar da duniya kan yadda ake yakar cutar CORONA da yadda za'a maganceta a duniya.
---Dr.Richard Bernan.
---
Daracta na kungiyar kiwon lafiyar kasa-da-kasa ta duniya (WHO) a yankin gabashin duniya,Dr,Richard Bernan ya bayyana Iran a matsayin kasar da yaga yadda ake yaki da cutar Korona din a zahiri.
Dr.Richard Ya bayyana cewar nan gaba kadan Iran ce zata zama kasar da zata ilimantar da duniya yadda ake magamce cutar Korona din.
Yace wannan shine karo na biyu da na ziyarci Tehran tun bayan barkewar wannan cutar,a gaskiya na ga yadda Iran ke da matukar karfi da hadin kai wajen yin tattalin matsaloli,kuma naga hadin kai wajen mutanen Iran wajen yakar wannan cutar.
-
Yace tun daga filin jirgin sama na fara sa ido sosai,naga wasu injina da na'urorin da aka girgirke domin tantance masu shigowa da fita domin a ga ko mutun yana dauke da cutar,ko wata cutar ma ta daban?
Yace,ba kamar a baya ba,yanzu muna iya cewar,Iran ta samu dubarun yin yaki da wannan cutar,don haka nan gaba dole Iran ta ilimantar da duniya hanyoyin yakar wannan kwayar cutar. Dr.Richard ya bayyana Iran da cewar,kasa ce ta daban wanda da gwamnatin kasar da al'ummarta ke yin aiki babu kakkautawa wajen yakar wannan cutar,kuma kowa na bada hadin kai kamar yadda ya dace. Don haka lallai Iran ta ciri tuta.
-
A wani labarin mai kama da wannan,wakilin kasar Iran a ofishin UN dake birnin Geneva Dr.Esmael Baghaei Hamaneh ya gana da Darakta Janar na WHO din na duniya Dr.Tedros Adhanom Ghereyesus a Genevan kan wannan matsalar ta CORONA,inda Daraktan WHO din ya gode wa kasar Iran, sannan ya nemi hadin kan Iran wajen yakar wannan cutar a duniya baki daya. Dr.Ghareyesus ya bayyana cewar, kullum yana karbar rahoto daga Iran,kuma yana farin ciki matuka game da cigaban da Iran ta samu a wannan fannin na kiwon lafiya,da kuma sabbin hanyoyi da dubarun da ta bullo dasu wajen yakar wannan Cutar. Yace Iran ta nazarci cutar COVID-19 cikin hikima,ilimi da kwarewa kuma ta samu ilimin yakar cutar,don haka yana rokon Iran da lallai duniya na bukatar hadin kanta wajen yakar wannan cutar.
----
Nasir Isa Ali
Tags:
Daga marubata