Sheikh Ibrahim Zakzaky (H).
Daga --Idishia Jos.
HAIHUWAN IMAM ALIYU DA TSATSON SA.
Kuma an haifeshi ne ranar Juma'a a watan Rajab shekara 30 bayan haihuwan Manzon Allah (S), Sayyida Aliyu ya kasance dane ga Abudalib Wanda asalin sunan sa Abdulmunaf, kuma mahaifiyarsa itace Fatimatu bin Asad bin Hashim kakansa shine Abdulmudallif bin Hashim. Da mahaifin Sayyidina Aliyu da mahaifin Manzon Allah (S) uwa daya ne uba daya ne Shakikai ne wa da kani ne dan haka kakan su daya ne kakan Manzon Allah shine kakan Sayyidina Aliyu (As).
Imam Aliyu (as) yana da 'yan uwa maza akwai Daleeb, Aqeel da Jafar sannan yana da 'Yan uwa mata da Ummu Hani da Jimada.
KAMALAN KAMANNIN SAYYIDINA ALIYU (AS)
Shi Imam Aliyu (As) ya kasance ba zaka ce mai dogo ba kuma ba gajere ba idanunsa manya ne yana da kwayar baki a idonsa, fuskansa tana da haske kamar hasken wata a daren lailatul badar sannan kuma ya kasance yana da siffa na karfi a jikinsa, wato shi ba siriri bane kuma sannan shi ba zaka ce mai yana da kaurin jiki wanda yayi yawa ba.
TUN ASALIN IMAM ALIYU (AS) MUSULMI NE.
tarihi ya nuna mana shine farkon Musulunta bayan Sayyidinatuna Khadija matar Manzon Allah (S), idan muna magana akan wannan babi ko magana akan asali to shi Sayyidina Aliyu (As) asalinsa shi musulmi ne an haifeshi shi tsarkakakke ne. Amma idan ana magana waye farkon musulunta to anan zamuce Sayyidina Aliyu shine farkon musulunta, duk da yake wasu na cewa a yara shine na farko, to shi musulunci a wajen Allah ba wani yaro ba wani babba in dai kayi imani da Allah (T).
MATAN SAYYIDINA ALIYU (AS) DA 'YA'YAN SA.
Daga cikin matan Sayyidina Aliyu (As) matarsa ta farko itace Sayyida Fatima (As) wanda kuma lokacin da ya aureta ya zauna da ita bai auro wata mata ba wanda ya hadasu tare ba, tarihi ya nuna a wannan gidane aka samu miji da mata a gidan ma'asumai. Mata ma'asumiyya miji ma'asumi to tun daga Annabi Adam (As) har izuwa Manzon karshe ba'a samu wanda yake miji da mata ma'asumai bane sai gidan Amirul-Muminin (As), kamar yadda muka sani Ayar "Tadihir" ta tsarkakesu.
Matarsa itace uwa ga Hassan Da Hussain da Ummu-Khulsum da Zainab da Muhsin. Sannan kuma Sayyidina Aliyu (As) yana da wasu mata wanda ya aura bayan ta akwai Khaula 'Yar Jafar Bin Khaisun Kas'amiyya, da Ummu-Habiba da Ummul-Banin da Laila Bintu Mas'ud da Asma'u Bintu Umais da kuma Ummu-Sa'id wadannan sune matansa. Yana da 'ya'ya Ashirin da bakwai (27), Maza Goma sha daya (11) mata su Goma sha shida (16).
A 'ya'yansa maza babbansu shine Imam Hassan almujtaba wanda Manzon Allah (S) ya ambace shi da 'Sibdil Akbar' sai mabiyinsa shine Imam Hussain (As) shahidin Karbala wanda Manzon Allah (S) yace Hassan da Hussain sune shuwagabannin samarin Aljanna. Sannan Muhammad wanda ake mishi alkunya da abul Kaseem, akwai Amru da Abbas da Jafar da Usman ance wannan Usman an sanyawa Usman bin Mas'ud ne a lokacin da ya zamo ya koma zuwa ga Allah sai Manzon Allah yace ya mai wasiya da ya sanya wannan suna. Akwai Abdullahi, Muhammad Asgar sannan Ubaidulla da Yahya.
'Ya'yansa mata akwai Zainabul-Khoubra da Zainab-Sugura da Rukayya da Ummul Hassan da Ramla da Nafisa da Rukayyatu-Sugura da Ummu-Hani da Ummu-Kiran da Jumana wacce ake mata alkunya da Ummu Jafar sai kuma Umama akwai Ummu-Salma da Maimuna da Khadija da Fatima, wadan nan sune 'ya'yansa mata.
ALKUNYA DA LAKABONIN SAYYIDINA ALIYU(As).
Ana mishi alkunya da Abul-Turab, Abul-Hassan ance imam Hussaini yakan kirashi da Abul-Hassan shi kuma Imam Hassan yana kiransa da Abul-Hussain, Su suka sanya mishi wannan suna. Sannan ana mishi alkunya da Abul-Subdain ko Abu-Raihanatain ko Abul-Turab wanda Manzon Allah (S) ya ambata, kuma shi ya sa mishi. Sannan yana da lakabobi da yawa wanda sun kai kimanin Dari da dauri, a wani kaulin Littafin Kawarizmi yace Sayyidina Aliyu yana da lakabobi wanda yake basu gaza Dari Takwas da Hamsin ba (850). Ana ce mishi Amirul Muminin shine kadai Amirul-muminin ko sauran A'imma ba'a ce musu Amirul-Muminin domin shi kadai ne Amirul-Muminin duk wanda ya kira kansa da wannan suna to ya sanya ne amma ba sunan shi bane, domin wannan suna Manzon Allah (S) shi ya sanya mishi.
Shi yasa ma a wani kaulin duk wanda yayi da'awan shine Amirul-Muminin wannan yayi karya domin Amirul-muminin shi kadai ne shine Sayyidina Aliyu (As), kuma wannan nassosi sun tabbatar domin duk wata Ayar Alkur'ani da tace "Ya Ayyu Hallazina Amanu" a cikin al'kur'ani to shi Sayyidina Aliyu (As) shine shugaban wannan "Allazina amanu" shine akan gaba. Akan mishi lakabi da Abul-A'imma, Khalilul Nubuwa, Almak'susu bil Ukuwa, akan mishi lakabi da Yasubul Iman, da Yasubul Din, akan mishi lakabi da Mizanul Iman domin shine ma'aunin aiki duk aikin mutum da zaiyi kyawawa in aka sa a sikeli aka ga ba son Aliyu to wannan aikin sukan zamo munanan aiki, domin son imam Aliyu shine yake tantance mumini da munafuki saboda haka duk kyawun aikin mutum in aka wayi gari zuciyarshi bata son Sayyidina Aliyu to wannan aiki ba zasu amfanar da shi ba.
KUSUSIYYA DA DARAJOJI NA SAYYIDINA ALIYU (As).
Shi Sayyidina Aliyu (As) yana da kususiyya da darajoji da aka ke be su da shi wanda babu wani a cikin wannan al'umma da yake da wannan kususiyya tashi saboda haka bayan Manzon Allah (S), in ka cire Manzon Allah a cikin wannan al'umma to babu wanda yake da Kususiyya da daraja da falaka na shi Sayyidina Aliyu (As). Na farko kamar yadda muka yi bayani an haifeshi a "Kaba'a" ba a haifi wani kafin shi ba, haka kuma bayansa ba a haifi wani ba. Sannan Manzon Allah ya had a 'Yan uwan taka da kowa, kowanne sahabi ya bashi abokin sa da aka zo kan Sayyidina Aliyu (As) yace ni wanene abokina Manzon Allah (S) yace "Anta Aki Fidduniya Wal Akira" kaine dan uwa na a duniya da lahira, saboda haka babu wani a cikin wannan al'umma da zaka ce dan uwan Manzon Allah (s) sai shi Sayyidina Aliyu (as).
Duk Inda Manzon Allah (S) zai je yaki Manzon Allah shi yake rike da tutarsa shine "Halimul liwa" na Manzon Allah (S) to haka ma zai kasance a ranar Lahira shine zai riki "Liwahil Hamdu" tutar yabo na Manzon Allah (S). To in an bashi zai bawa Sayyidina Aliyu ne suna karkashin al'arshi. Kuma sannan Manzon Allah bai taba sanya wani shigaba akan shi ba, amma shi ya shigabantar da shi akan sauran sahabbai saboda haka babu wani sahabi da ya shigabanci Sayyidina Aliyu.
Sannan runutun zobensa shine "Allahul Malik Wa Aliyu Abdahu" yayi man yan yakoki a rayuwansa guda uku da Jamal da Siffin da Nahrawan. Sannan tutarsa itace tutar Manzon Allah (S). Mai maa hiidima shine Salmanul Farisi, marubucinsa shine Abdullahi bin Abirafi.
SHAHADAN SAYYIDINA ALIYU (AS) DA INDA AKA BINNESHI.
An binne imam Aliyu a Najaf can kasar iraki wanda yayi shadaha a ranar 21 ga Ramadan,
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
#FreeZakzaky
Tags:
Jawaban Malamai