Bature ne ya assasa mana mulkin ƙasƙantattu!



Ma'asumah Nigerian News Update

Nktw: Bin Haroun Sigau

(Turawa) Da ma su suka dauko mutanen (nan da ke mulki) suka ajiye, daga mai abin kunya anan, sai wanda da can yana saurayi ya taba satar Akuya, sai wanda a lokacin da yake Sakandire ya sace Keken mai gadi. Eh!Sosai sune gwamnonin mu, kowa ka bincika sai ka ga abin tsiya a tare da shi. Dama sai laluba sun samo lalatacce, sai su ce shi ne wakilinku, wadansun ma da yawa yan zina, sunc wakilanku, in ba dan zina ba, imma yana da uba, ya bar gidan uban.

Ko sun bata da uban ko uban ya tsine masa. To shi ne suka debowa su daura a matsayin wakilai sune zasu wakilce ku. Saboda haka su bai ma dame su ba meke faruwa, kowanne ma zaka ga shi bai dame shi ba, shi abinda ya dame shi kawai, shi me zai samu, abin da yake da bukata, shi za a tattara masa a ba shi, shikenan.

In mashayi ne a tattara masa, abin sha. In mazinaci ne, a tattara mishi, in dan Luwadi ne a tattara mishi, shikenan kawai, su abin da ya dame su. Irin wadannan su suke zabowa, ya zama wakilcin al'ummah ya kau ma yanzu, yanzu ba batun, kuna iya ganin cewa in an siyasar farko, har an yi zabe, an yi'One-Man One-Vote' yanzu an tashi awannan marhalar.

Yanzu ba ainahin mutane ke zabe ba. Ana dankarawa ne, kuma su suke dauko wanda za su dankara, sun hana a yi
jam'iya, su suke muku jam'iyya, sun hana a tsayar da dan takara, su suke tsayar da dan takara, sun hana a yi zabe, su suke Zabe. In ku ka yi jam'iyya, sai su ki yi mata rijista, sai su muku Jam'iyya, in ku ka yi rijista, sai ku shigo jami'iyar su da suka yi.


In kuka tsayar da dan takara, sai su ki yarda, sai su tsayar muku da dan takara, in ku ka ce to shikenan yanzu to a cikin wadannan da ku ka tsayar mana din, mu zabi wani man, sai su kuma su hana ku, sai su zaba muku wani. Haka yanzu ake sannan kuma a ce yauwa, Dimokradiyya kun kun zabi Shugaba, shikenan.

–Sayyid Zakzaky (H) a wajen taron da yan uwa daliban makarantar Boko, da hadin guiwar yan uwa  mata suka shirya a garin Katsina. 1439-Hijriyya, daidai da 2018 Mikadiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post