Batun Hana Bara: Bai Dace Malamai Su Kalubalanci Gwamna Ganduje Ba- Pantami

Isa Ali Pantami cewa yayi Bara ba addini bane kuma bai zama wajibi ba.

  Daga wakilin Shafin Ma'asumah --Idishia Jos.

Ana tsaka da cigaba da cece-kuce akan batun hana yin bara a Kano, wanda jihar ta haramta a wannan mako da muke ciki, kwatsam sai aka jiyo Minisatan Harkokin Sadarwa da kuma sabon tsarin tattali na zamani, Dakta Isa Ali Pantami, yana bayyana aibun matsayin da wasu Malami suka dauka na yin watsi da wannan matsayi wanda Gwamnatin Jihar Kanon ta dauka, inda ya bayyana cewa ba daidai ba ne kalubalantar Gwamna Ganduje akan wannan al’amari, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar LEADERSHIP A ranar Lahadi.

Ministan na yin wannan tsokaci ne, a lokacin da yake amsa tambayoyin mane ma Labarai jim kadan bayan kammala gabatar da takardar da ya yi a lokacin bikin yaye daliban da Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano Polytechnic), ta gudanar a sashin makarantar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Abinda na ke cewa akan wannan batu shi ne, ba daidai ba ne ga ‘yan’uwana Malaman Addinin Musulunci, su cigaba da kalubalantar Gwamna Ganduje haka kurum. Kamata ya yi su zo su zauna, domin samar da mafita ta yadda za a aiwatar da tsarin tare da magance halin da ake ciki,” Dakta Pantami ya kuma bukaci cewa, “kasancewa babu ko tantama mayar da wadancan yara makaranta shi ne abinda ya fi dacewa, sannan kuma shi ne zai amfani Almajiran, iyayensu da kuma al’umma baki-daya. A bangaren Gwamnati

kuma, kasancewarka Shugaba akwai hakkin da rataya a wuyanka na ganin cewa, al’umma sun samu rayuwa mai kyau kwarai da gaske.” Saboda haka, sai ya bukaci Malamai da su fahimci cewa, idan akwai mai wani abu da ya kamata a yi, kamata ya yi a samar da hanyar zama, domin tattaunawa tare da samar da hanyar warware matsalar baki-daya. “Wannan kawai shawara ce” a cewar tasa. Har ila yau, Pantami ya nuna sha’awarsa ta kasancewa cikin wadanda za su gudanar da wannan tattaunawa, musamman idan aka samar da wani Kwamiti wanda zai tattauna cikakken batun, “ina fatan kasancewa a cikin wadanda za a yi wannan tattaunawa da shi, idan bukatar hakan ta taso.”

Sannan ya kalubalanci kowa da cewa, “dukkaninmu muna da yara, ni nawa yaran suna nan tare da ni, ina kuma jin su tamkar wani bangare ne na jikina. Kun san ciyar da yara hakki ne da ya rayata a wuyan iyaye, idan akwai marayu wannan mun san yadda al’umma ke lura da su, kuma suke yin la’akari da halin rayuwar da suke ciki. Don haka, ni na taso a gaban iyayena, na ga yadda iyayen nawa kuma ke ciyar da marayu tare da kula da lafiyarsu.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. J

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post