@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
QIYAYYARSA GA ANNABI (S.A.W.W)A BAYYANE TAKE
A bakinsu za su nuna maka su suka fi kowa son Annabi (S.A.W.W)da kuma yin koyi da sunnansa.
Aikin mutum shi ke fassara ko shi waye a haqiqa, domin da ace furuci shine ma'auni na sani mutum, to, da munafukan zamanin Manzon Allah (S.A.W.W)sun sami mafaka, kuma da ba a bayyanar da halayyarsu cikin Qur'ani don a sansu ba.
Maulidin Manzon Allah (S.A.W.W)ya zama babban ma'auni na sanin masoyansa da kuma maqiyansa (S.A.W.W).
Za ka sami dan Izala na nuna matuqar qiyayyarsa ga yabon Annabi da ake yi , ko da kuwa babu kida cikin wannan yabo.
A shari'ar muslimci akwai irin wannan kida da ake yi don nuna farin ciki na samuwar wata ni'ima, kuma duk wata cikar ni'ima ba ta kai ta samuwar fiyayyen halitta (S.A.W.W)ba.
YADDA AKE GANE HAKA
Za ka same su da yawan sauraren waqoqin siyasa, su hada kai suna saurare har ma da raha da nuna nishadinsu a bayyane.
Abinda zai ba ka makaki shine, cikin wayoyinsu za ka sami mafi yawan vidios da ke ciki kida-kide ne da rawa wadanda mata ke yi.
Ba ma matan musulmai wadanda za sanya sutura irin tamu ta hausawa ba, a'a, irin na turawan nanne da indians masu barin mafi yawan jikinsu a waje.
Har malaman cikinsu na kallo da sauraren irin wadannan abubuwa, amma ba sa ganinsu a matsayin laifi.
Laifi shine, waqoqin yabon Manzon Allah (S.A.W.W)wanda ake yi. Idan ka qalubalence su sai suce ai irin kida-daden da suke saurare suna yi ne a matsayin nisadi ba wai da sunan addini ba.
Wai shi kuma wanda ake yi na yabon Annabi (S.A.W.W)ana yinsa ne da sunan addini, alhali ba addini bane.
YAA ALLAH KA RABA MU DA MAQIYA MANZON ALLAH (S.A.W.W)!
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~28th March, 2020.
Tags:
Daga marubata