Aqida: Matsayar manyan maluman Shi'a dangane da ƴan Gullatu




MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

–Bin Haroun Sigau

Hakika manyan malumman Mazhabar Ahlulbaiti (a.s) sun dauki bayyanan ne kana fitaccen matsayi dangane da wannan yunkuri na 'yan Gullatu, suna masu dogara da hadisan da suka zo daga Imaman Ahlulbaiti (a.s), inda dukkan su suka tafi a kan barranta daga wadannan munanan maganganu na su da kuma la'antar su kan hakan, sannan da kuma bayyanar da karya da rashin gaskiyar su kan wannan al'amari. Hakan kuwa ya zo ne cikin littattafan su na akida da dai sauransu. Don haka ga kadan daga cikin irin wadannan maganganu na su:

Shaikh Saduk (r.a) yana cewa: "Akidar mu kan 'yan Gullatu da 'yan Mufawwida (masu cewa Allah ba shi da wani iko ko hannu cikin ayyukan bayin sa) itace cewa su sun kafirce wa Allah Madaukakin Sarki, kana kuma su sun fi sharri a kan Yahudawa, Nasara, Majusawa...da dai sauran kungiyoyin bid'a da bata".

Shi kuwa Shaik al-Mufid cewa yake: "yan Gullatu
suna daga cikin masu ikirarin Musulunci, sune suka jingina Ubangijintaka da kuma annabtaka ga Amirul Muminin da Imamai daga zuriyar sa (a.s)....su batattu ne kuma kafirai, Amirul Muminin (a.s) yayi hukumcin kisa a kansu da kuma kona su da wuta, su kuwa Imamai (a.s) sun hukumta su da kafirci da kuma fita daga Musulunci).

Shaikh Muzaffar yana cewa: "Ba mu yi imani game da Imamai (a.s) irin yadda 'yan Gullatu masu wuce iyaka suka yi ba, haka nan ba mu yi irin yadda 'yan Halluyuna (masu cewa "Ruhin Ubangiji" ya sauka a jikin Imamai) suka yi ba (kalmar da ke fita a bakunan su ta girmama). "Mu imanin mu a kebe shi ne cewa; su mutane ne kamar mu su na da abin da muke da shi, kuma abin da yake kanmu yana kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa, Allah Ya kebance su da karamar sa kuma Ya so su da soyayyar sa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, takawa, jarumta, karimci, kamewa da dai sauran kyawawan dabi'u mafifita na daga kyawawan siffofi
kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.

Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Duk abin da ya zo muku daga gare mu wanda ya halatta ya zamanto daga halittu, kuma ba ku san shi ba, ba ku kuma fahince shi ba, to kada ku musa shi ku mayar da shi gare mu, kuma abin da ya zo muku daga abin da bai halatta ya kasance daga halittu ba ku musa shi kuma kada ku mayar da shi gare mu"

Shi kuwa Shaikh Kashiful Ghita, yayin da yake magana kan 'yan Gullatu da kuma maganganun su cewa yayi: "Amma Shi'a Imamiyya da kuma Imaman su (a.s) sun barranta daga wannan kungiya...Sun barranta daga wadannan maganganu na su, kana kuma suna kirga su a matsayin mafi munin kafirci da kuma bata, don kuwa addinin su (a.s) bai kasance ba face kadaita Allah Shi kadai, da kuma nesantar da Mahalicci daga dukkan wata siffa ta halittu..."

Don karin bayani a duba
1. Aka'id Imamiyya na Shaikh Muzaffar: 326/28, Akidatuna fil A'immah (As), Muassasat Imam Ali (As) birnin Kum bugu na daya.
2. Aslush Shi'a wa Usuliha na Shaikh Kashiful Ghita 173-177, Muassasat Imam Ali (a.s) - birnin Kum, bugu na farko.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post