Batanci Ga Annabi:An Yi Zanga-zanga A Kano Kan Kalaman Batanci Ga Annabi(S.A.W).
Rahotanni daga Kano a Najeriya,sun nuna cewa dandazon matasa sun yi tattaki zuwa ofishin hukumar Hisba dake jihar Kano domin nuna bacin ran su kan kalaman batanci da wani dan Hakika ya yi kan Manzon Allah (S.A.W)
Mai magana da yawun matasa masu zanga-zangar, Ibrahim Idris wanda aka fi sani da Baba Idris, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da aka yi 6atanci ga Annabi SAW a Kano, don haka akwai bukatar a soma daukar matakin gaggawa ga masu irin wannan mummunar akidar.
Idan ba a manta ba dai, a makon da ya gabata ne wani matashi da ke Unguwar Sharifai a cikin birnin Kano mai suna Yahaya Sharif Aminu ya yi kalaman batanci ga Annabi SAW a wata waka da ya fitar, inda har ta kai ga mafusata sun rusa gidansu

Tags:
Labaran Duniya