Kotun shari’a ta kafur tayi ma wasu mutane (7) mata da suka mallaki hankalinsu bulala (30) sakamakon kamasu cikin maye da akayi a mashayar unguwar shaka fada dake cikin karamar hukumar kafur.
Daga -Idishia Jos.
'Dan sanda mai gabatara da kara sajen Murtala Yakubu yace an shigar da karar ne a tsakanin kwamishinan ‘yan sanda da mutane (7) wanda laifin da ake zarginsu da aikatawa ya sabama kundin doka sashi na (366) na kotun shari’a na jihar Katsina.
Mai shari’a Malam Ayuba Yahaya ya karanta laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa wadanda dukansu sun amince ya kuma zartar masu da hukuncin bulala (30) ga kowannensu ba tare da zabin biyan tara ba. Malam Ayuba Yahaya yace wadanda aka yima hukuncin sun hada da Bilkisu Sani, Aisha Abdullahi, Hafsat Bala, Talatu Ibrahim, Maimuna Ibrahim da Rabi’u Hasan dukkansu dake a garin kafur.
Ya bayyana cewa an kama masu laifin ne sannan kuma aka mikasu kotu bayan kammala binciken ‘yan sanda. Haka kuma an tura wani mai suna Aminu Audu dake kauyen dan Amarya a karamar hukumar kafur gidan yari bisa zargin da aka yi mashi na Sarema akuya kafaunta da ranta wanda hakan yayi sanadiyyar yankata. dan sandan mai gabatar da kara Sajent Murtala Yakubu ya shaidama Kotu cewa wanda ake zargin yace akuyar tayi mashi barna a lambun kayan miya shiyasa ya dauki wannan mataki. Abiyo mu sati na gaba domin jin karashen yadda ta kaya a kotunan.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya