An Sace Fasfon Mai Yunkurin Zuwa Makkah A Keke

Babban magana tun kafin ya bar Nigeriya an fara samun matsala.

Daga --Idishia Jos.

A wannan mako da mu ke ciki ne, wani dan asalin Jihar Filato, Malam Aliyu Abdullahi Obobo, ya shirya tsaf ya kuma kama hanya a kan keken hawansa zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali. Amma sai dai bayan kwanaki hudu da barowarsa Jos zuwa Jihar Kano ne, ya gamu da wani iftila’i na haduwa da wadansu bata-gari, wadanda su ka bata ma sa wannan tafiya da ya kudiri niyyar yi, ta hanyar sace ma sa fasfon din da zai ba shi damar shiga wannan kasa Mai Tsarki.

Kamar yadda Aliyu Abdullahi ya bayyanawa manema labarai, ya ce, wannan tafiya tasa ta samo asali ne daga yawan mafarkai da yake faman yi na zuwa kasar ta Saudiyya akai-akai. Saboda haka, wannan dalili ne yasa shi ya kudiri niyyar yin wannan tafiya domin cika al’kawari ko dai a jirgin sama ko kuma akan keken da Allah Ya hore masa.

Ya cigaba da cewa, bayan isowarsa Kano ne, sai ya tsaya a wani wuri domin kewayawa bayan gari ya biya bukatarsa ta dan Adam, kwatsam sai ga wasu Matasa sun tunkaro shi tare da tambayar sa cewa, mene ne wannan? Kafin dai ya ankara, tuni sun wafce jakar da ke hannunsa sun arce. Inda wannan al’amari a halin yanzu ya sanya shi cikin tsaka-mai-wuya, yake kuma rokon Allah Ya yi ikonsa da Ya saba yi; domin cika masa wannan babban buri nasa.

Tunda farko dai, Malam Aliyu ya bayyana kudirin da ya yi na kasancewa a cikin kasa mai tsarki nan da watanni biyu da sati biyu cif akan wannan keke nasa, musamman da ya ji cewa Hukumomin Saudiyya sun hana shiga kasar sakamakon Cutar Makoshi ta Cobid-19. Saboda haka, zai so ya yi amfani da wannan dama domin gode wa Sarkin na Makkah akan wannan kokari nasa na daukar wannan mataki, don kare wannan kasa mai tsarki daga wannan cuta.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post