AN GUDANAR DA GAGGARUMAR MUZAHARAR FREE ZAKZAKY YAU A KANO

*BA'A BAMU TSORO DA KISA KAWAI A SAU SAYYID:


Taken Muzaharar yau kenan a Kano

@Ma'asuma Nigeria News Updates

Yau ma kamar kowane lokaci Yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky na Garin Kano. Sun sake fitowa akan kwalta a tsakiyar Birnin Kano. Suna masu kara shelantawa duniya cewa lallai dole a saki Shehin Malamin nasu.

Sai dai Muzaharar ta samu halartar matasa muzaharar. Inda muzaharar ta fara ne, da misalin karfe 2:00pm na ranar. A yau talata 31/3/2020 , saka makon halin da akaji su Sayyid Zakzaky da Mai Dakin da. Suke ciki a Babban Kurkukun da ake tsare da su a garin Kaduna.


Sai dai Muzaharar ta dauki dogon lokaci ana gudanar da ita. Inda aka kammala muzaharar ta yau a karkashin gadar Yan kura da ke a cikin garin Kano.



Daga wakilinmu:
Auwal M Tukur
31/3/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post