Amurka Ta Shige Gaba Wajen Yawan Wadanda suka Kamu Da Corona

Kididdiga ta nuna cewa Amurka ce kan gaba a halin yanzu wajen yawan wadanda suka kam da cutar corona.

(ROHOTON ABNA24.com) Kamfanin dillancin labara Anatoli ya bayar da rahoon cewa, bisa ga alkalumman da jami’ar Johns Hopkins ta kasar Aurka ta bayar, adadin wadanda suka kamu da cutar corona a Amurka a halin yanzu ya wuce na kasashen Italiya da China.

Jami’ar ta ce a halin yanzu Amurka da mutane dubu 85 da 653 da suka kamu da cutar corona, yayin da China take da dubu 81 da 782, sakuma Italiya take biye mata da dubu 80 da 589.

Ya zuwa ranar Ahamis mutane 1,178 ne cutar corona ta kashe a kasar Amurka.

Ita ma tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, ranar Alhamis da ta gabata ita ce rana mafi muni, wadda corona ta kashe mutane 248 a kasar Amurka.

Ya zuwa yanzu dai mutane fiye da dubu 531 suka kamu da cutar corona a duniya, yayin da fiye da dubu 23 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post