Allah ya nunawa Annabi (S.AWW) abinda zai faru ga Imam Ali (AS) a bayan Sa!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KAN HAKA YA YI KUKA (S.A.W.W)

Duk wani abinda tarihi ya kawo na abubuwan da suka faru ga Imam Ali (A.S)na cutarwa da qiyayya bai buya ga Annabi (S.A.W.W)ba, domin Allah (T)ya nuna masa tun kafin wafatinsa.

Saboda haka ba zai zama abin mamaki gare mu ba, kuma ba abune wanda wasu za suyi qoqarin lullube shi ko wanke wadanda suka cutar da shi (A.S)ba.

An karbo daga baban Usman An-Nahdiy, daga Aliyu (K.W)yace,

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W)yana riqe da hannuna muna tafiya cikin sashen unguwannin Madinah, sai muka je kan wata gona (Lambu), yace, sai nace; ‘’ Yaa Ma'aikin Allah, menene yafi kyau daga wannan lambu ?‘’

Yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ABINDA YAFI KYAU CIKINTA KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU A ALJANNAH .‘’

‘’ Sa'an nan muka qara shudewa kan wata (Lambu)na dabam, sai nace;Yaa Ma'aikin Allah, menene yafi kyau daga lambun nan ?‘’

Yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ABINDA YAFI KYAU KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU A ALJANNAH !‘’

‘’ Har dai sai da muka shude kan lambuna (gardens)bakwai, kowannensu ina cewa wanne abu ne yafi kyau cikinsa, kuma yana cewa; ‘’ KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU CIKIN ALJANNAH .‘’

To, a yayin da muka kebe da shi akan hanya sai ya rungumeni, sannan ya fashe da kuka (He burst into tears)!Sai nace, Yaa Ma'aikin Allah, kukan me kake yi?Yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ QIYAYYARKA CE KAWAI CIKIN ZUKATAN MUTANE, AMMA BA ZA SU NUNA MAKA BA HAR SAI BAYAN RASUWATA .‘’ Yace,

‘’ Sai nace, Yaa Ma'aijin Allah, ince dai akwai aminci cikin addinina ?‘’ Yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ AKWAI AMINCI CIKIN ADDININKA !‘’

(Nurul-Absar, Sh:129)

Saboda haka duk wanda ka ji ance ya ja da Imam Ali (A.S)bayan wafatin Annabi (S.A.W.W), to, wannan qiyayyar ce ya bayyanar da ita, kuma munafuki ne ko shi waye !

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~22nd March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post