Akhlaq: Fa'idar girmama wanda ke sama da kai a shekaru!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SHI KUWA JAHILI BA YA FAHINTAR HAKA

Na kasa sanin haqiqanin wannan magana, shin hadisi ne ko kuma dai karin magana ce irin ta ma'abota hikima?

Za ka ji ana cewa, ‘’ BIN NA GABA BIN ALLAH .‘’

To, ko ma menene dai wannan magana tana da ma'ana, kuma ba ta ci karo da na wani nassi na aya ko hadisi ba.

Sai dai duk da haka sai ka tarar wasu ba su san girman na sama dasu a shekaru ba ballantana kuma ace sun san girma da darajar wanda ma ya haife su a al'adance. Har ma ka ji suna cewa, ‘’ IDAN SA'AN BABANA NE AI BA BABAN NAWA BANE !‘’

Ma'ana, ai ba shi ya haife su ba a tunani irin nasu da har za suga girmansa. Su irin jinsin wadannan mutane za ka tarar da su jahilci ya yi katutu cikin qwaqwalwarsu, shi yasa ba su san shekaru wani abu bane abin girmamawa.

Kuma da za ka bibiyi tarihin irinsu sai ka tarar har mahaifan nasu ma da suka haife su ba sa ganin girmansu, rashin ganin girman mahaifan nasu ne ma yasa ba za su taba ganin girman wani ba.

Yin haka kuwa ya sabawa koyarwar dukkan wata da'awa ta muslumci, domin Annabi (S.A.W.W)bai koyar damu yin haka ba.

Cikin dabi'unsa kyawawa (S.A.W.W)ya kasance mai girmama duk wanda ke sama da shi, ko da kuwa shi ba musulmi bane. Irin wannan kyawawan dabi'u nasa (S.A.W.W)yasa da dama suka gaskata shi  yayin da ya soma yin kiran dawowa kan addinin Allah (T).

Daga cikin fa'idar da ake samu ta hanyar girmama wanda ya fi ka shekaru shine, ya zo cikin wani hadisin Ma'aiki (S.A.W.W)inda yake cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ MATASHI BA ZAI TABA GIRMAMA TSOHO SABODA SHEKARUNSA BA FACE ALLAH YA TAYAR DA WANDA ZAI GIRMAMA SHI YAYI SHEKARUNSA (na tsufa).‘’

To, idan kuwa hakane, duk wani matashi ko matashiya da ba sa girmama wanda ya fi su a shekaru ba, lalle a qarshen rayuwarsu ta tsufa ba za su sami masu girmama su ba in ba 'yan iska lalatattu irinsu ba, domin hausawa na cewa;

‘’ KO A GIDAN GIYA MA AKWAI BABBA (wanda ake ganin girmansa).‘’

Amma ai kowa ya san girman gidan giya girman banza ne.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

09039791509-08126385470

~2nd March, 2020.

            F  R  E  E

                    O
                    U
                    R

        L  E  A  D  E  R

S
     A
          Y
              Y
                   I
                         D   

 ZAKZAKY  (H)!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post