*@MA'ASUMIYA NIGERIAN NEWS UPDATE@*.
TARON KARAWA JUNA SANI
*_____MAI TAKEN_____*
"YAUSHE ZAMU FARKA".
__________________
ABIDI AMINU.
A safiyar ranar Assabar 14/March/2020 ne Kwamitin Joint Fora karkashin Jagorancin Allamah Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) suka shirya gagarumin mu'utamar na wuni daya a garin Talata Mafara ta Jahar Zamfara mai taken *"YAUSHE ZAMU FARKA"*.
Wannan Mu'utamar dai ya samo asalii ne dalilin Yunkurin Farkar da yan uwa akan al'amarin nemawa Jagora 'Yanci, Wanda akafi sani da Abuja Struggle.
Shi dai Mu'utamar din na wuni daya ya samu halartar manyan Malaman Harka Islamiyya na bangarori daban daban, Tun daga kan Sheikh Rabi'u Funtua, Sheikh Sidi Munir Sokoto, da Kuma Sheikh Dr Sanusi Abdulqadir Kano, da wasu Wakilan Da'irorin yankin Sakkwato Zamfara Kebbi.
An gudanar da Jawabi biyar ne a taron (kamar yanda ya zamo al'ada ta mu'utamar) a maudu'ai mabambanta wanda suke da muhimmanci dan gwagwarmaya ya tuna dasu a koda yaushe.
Mal Salisu Maradun daya daga cikin jajirtattun yan gwagwarmayar Abuja shine yafara gabatar da jawabi a maudu'i mai Taken "HAKKOKIN JAGORA", inda ya kawo bayanin sheikh dan fodiyo akan hakkon jagora a cikin gamsasshen Jawabinsa.
Mai Jawabi na biyu Shine Sheikh Sid Munir Sakkwati, wanda yay bayanai masu ratsa jiki a maudu'in "WAJABCIN TAIMAKAWA ABUJA STRUGGLE".
Bayan an dawo daga Sallah da kalaci Sheikh Rabi'u Funtua ya gabatar da jawabi akan "SHI'A BA GWAGWARMAYA SABON SALON YAQAR SAYYID (H)" kuma yayi gwala-gwalan jawabai akan haka.
Jawabi Na hudu Sheikh Dr Sunusi Abdulqadir Koki Kano shine wanda ya gabatar dashi, jawabi ne da kowa yake buqatar ya saurareshi akan "SABABBIN HANYOYIN TALLAFAWA ABUJA STRUGGLE", lallai duk wanda ya saurara zai qaro akai.
Mal Ayatullah Muhammad Abubakar Mainasm shine ya rufe bagiren jawaban taron da ta'aliqinsa akan halin da ake ciki a Abuja Struggle da kuma yanda ya kamata dan Abuja Struggle yayi tunani a rayuwarsa kaco kaf, musamman akan Wannan yaqin ruwan sanyin na kwakwalwa da mukeyi da Jahiliyya.
An tashi taron Lafiya tare da Fatan Alkairi.
Allah yasa mahalarta taron dama wanda basu samu halarta ba su amfanu ta hanyar yin aiki da abinda suka samu a wannan taron Qarawa Juna Sani din.
15/March/2020.