*ABINDA YA FARU DA NI JIYA ASABAR DA DARE MISALIN KARFE 8:30PM*
~Auwal M Tukur
A jiya Asabar da misalin karfe 8:30 na dare. Na fita daga chemist din mu domin naje na ci abinci. Sai nabi ta layin Malamai dake bayan gidan Isiyaka Rabi'u a cikin Birnin Kano. Kwatsam bayan da na gama cin abincin sai na biyo ta wannan layin domin komawa chemist din mu da ke a unguwar. Na zo dai dai kan layin na Malamai a saiti da transformer. Kawai sai na ga mutane dauke da sanduna da karafuna. Mutane suna ta gudu a layin. Sai nima na juya da gudu, domin na samu na tsira. Lokacin da ne muka samu muka shiga cikin Masallacin Isiyaka Rabi'u. Sai ake tambayar miye yake faru ? Shine sai wasu suke cewa ai Masu jihadi ne suka sake dawowa. Sunce sai sun kashe Malamin yaron da ya yiyi batanci ga Fiyayen Halitta (S.A.W). To a nan sai sauran yan Hakika da suke cikin Masallacin Isiyaka Rabi'u suka fara karyo itace da nemo karafuna na duka. Wasu har da Manjagara da adduna, wasu da duwarwatsu. Wasu suke cewa muma wallahi sai mun kashesu. Duk sai aka sake tinkarar inda wadancen masu jihadin suke,kamar yadda suka kira kansu da hakan.
To Nima ganin hakan yasa na bi domin samo rahoto. Kuma ko ba komai dama hanya tace da zan koma chemist din mu. Ai kuwa da isata a wurin na tarar da an zagaye wani mai mota ana cewa tare da su yake. Ana kokarin fara dukan sa. Sai wani dan sanda yake cewa ai tare suke. A kace dole sai sun juya. Kwatsam a bisa tsautsayi sai na fitar da wayana domin na dauki hoto. Nayi na farko ba flashlight, kawai sai na kunnan flashlight a na biyu. Ina dannawa flash din ya kawo. Sai naji wani Mai karfi ya rikeni yan cemin "uban miye zakayi da hoton. Munafuki, sai ka goge shi ka nayi ma dukan tsiya." Kafin na ankara duk matasane sun zagaye ni,da sanduna wasu da karafuna. Sai na fitar da I D card din na domin na nuna masa aikina. Sai yake cemin sai fa ka gogeshi ko kuma nayi na kwace wayar. Sai nace masa to bari na goge. Ina shiga galary sai na hango hotunan Yan uwa a ciki. Sai yake cewa shege Dan Shi'a ne. Ai sai na ji saukar mari a fuska ta. Sai yace a daina marina amma sai na goge hotunan. To a ciki a kwai hotunan rikicin tin na safe da aka fara a unguwar Dabai. Aka ce har su sai na goge sai kuwa na goge su. Sai yake cewa ku bani sanda wallahi sai na zaneka. Sai nake cemasa haba bayan na goge din ? Wallahi kawai na naji Matasan sun fara kawo min duka ta ko ina. Sai kawai fara kokarin na samu hanya na fita da gudu. Ai kuwa duk inda nayi sai dai naji saukar duka. Haka dai na samu na fara gudu, kawai sai ji nayi wani na bugamin sanda sai na kara gudu. To lokacin da suka ga Ina kokarin tsere musu shine wani ya Kara min kafar sa na Fadi. Sai sanduna da duka a fuska ta ko ina. Sai naji suna kokarin fin karfina shine na yunkura na jawo wani karamin generator na wurga musu. Sai duk suka watsi. A lokacin ne na kara basu tazara a tsakanin na dasu. To a lokacin akwai I'D Card dina a hannuna dayan hannun kuma waya tace a rike. Sai ga wani bawan Allah ganin I'D Card din a hannuna. Sai yake ce musu kai Dan sanda ne. Ku kyale shi , sai nayi kokarin na kai wurin sa. Sai nayi wani ya fusgi wayata. Sai na kara rike ta har nakai wurin wancen bawan Allah. Sai nace Malam ni ba Dan sanda ne ba, amma Dan Jarida ne.
To Jin hakan sai yayi kokarin turani a cikin gidan su. Sai ya kulle gidan, ya debo min ruwa. To a lokacin ne, na kiyaye da jini ne. Yake ta fitowa a bakina, da hancin na. Sannan Kuma duk a hannuna inda na Fadi Shima naji ciwo sosai. To a nan ne fa hankalina ya fara dawowa a gareni. Amma duk dai ban samu natsuwa da wurin ba. Sai shi wannan Bawan Allah yake tambaya cewa ma'aikiacin wane gidan rediyon ne ni ko Jarida ? Sai nake ce masa wani shafin Jarida ne Mai suna *Ma'asuma Nigeria News Updates* dake da a yanar gizo. Sai yake cemin to yanzu kana so ne na baka bayanin abinda ya faru. Sai nake ce masa ehh! Amma yanzu ka bari gaskiya sai gobe. Saboda yanzu ba a hayyaci nake ba. Amma gobe zan dawo. Nake ce Masa nan ne gidan ku ko? Sai ya ce min ehh! Nace to ya sunan ka ? Yace min Usman. Nace to ba komai gobe insha Allah zan dawo. Sai kayece min amma dai ba wani damuwa ko? Nace kamar na miye ? Yace kamar a jikin ka ko? Na ce a'a. Sai ya bude kofar ya leka domin ganin ko wayancen da suka biyo nin sun tafi kokuwa. Sai kawai muka ga ana ta wani sabon gudu. Cewa Yan Sandan ne suka zo. Sai yace min to kabi tanan kawai ka tafi abinka. Amma Kar kayi gudu. Nace ba komai na gode. Haka kuwa na bi ta inda ya nunamin. Har na koma chemist din mu.
Bayan da na karasa chemist din shine sai. Dayan abokin aiki ma yayi min treatment. Yan cikin wanke wurin da naji ciwon. Sai ga mutane a layin kuma suna ta gudu. Da aka tambaye su lafiya ? Shine suke cewa ai Masu jihadin ne suka farma gidan Malamin Wancen Matashin Dan gidan Limamin Unguwar Dabai Mai suna *SHEHI* da yayi batanci ga Manzon Allah. Amma yanzu Yan Sandan ne suke ta harba Barkon tsohuwa (Teagas) , a wurin.
Wannan shine abinda ya faru da ni jiya Assabar 28/ 3/ 2020. A Unguwar Kofar Waika, layin Malamai dake bayan gidan Isiyaka Rabi'u.

Tags:
Game damu