​Zarif: Hanya Mafi Dacewa Wajen Kare Kasa Ita Ce Fitowa Zabe karanta anan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya yi kira ga mutanen kasar Iran da su fito domin kada kuri’unsu a zaben majalisar dokokin kasar karo na 11, wanda za’a gudanar a gobe Jumma’a.

KARANTA WASU LABARAI ANAN 
(MAASUMAH.COM.NGMinistan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya yi kira ga mutanen kasar Iran da su fito domin kada kuri’unsu a zaben majalisar dokokin kasar karo na 11, wanda za’a gudanar a gobe Jumma’a.

Tashar talabijin ta Al-alam ta nakalto Zarif yana fadar haka a jiya Labara bayan kammala taron majalisar ministocin kasar a fadar shugaban kasa.

Ministan ya kara da cewa; kamar yadda mutane suka fito jana’izar Shaheed Sulamani domin kare kasar da kuma nuna goyon bayan ga tsarin siyasar kasar, hanya mafi dacewa ta nuna wannan goyon baya a halin yanzu ita ce fitowa domin kada kuri’a a zaben majalisar dokokin kasar mai zuwa.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Zarif ya bayyana cewa fitowa don zaben yan majalisar dokokin kasar zai kara tabbatar wa makiya kasar matsayin al’ummar kasar dangane da tsarin gwamnatin kasarsu.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post