@MA'SUMAH NIGERIA NEWS UPDATE
WAKILINMU:: Ammar Abubakar shadow
Hakika maganar gaskiya yan kidnapping suna abunda sukeso a arewacin Nigeria. Saboda idan ka natsu zaka gane cewa yanzu talaka ko ince Dan arewa ya sayar da yancinshi ga gomnati.
Kuma hakan ta farune saboda yanayin halinda aka jefa Al,umma a ciki sai ya zamana gabadaya mutane sun maida hankalinsu ga tsaro da abinci Kuma sunyi wuya ..
Mu kalli yankin B/gwari a koda yaushe ana fashi bisa hanya abiyo mutun har gida a kashe akama mata ayimasu fyade gaban maigidan wannan ya faru yafi a kirga..
Yanzu haka maganar nan danike hanyar B/gwari Bata biyuwa saboda yan kidnapping amma ahaka wasu zasu sadaukar da ransu su fita su dauki fasinja subi hanyar saboda basuda wata hanya data wuce sudau mutane su kaisu wani garin wato(driving)..
Kuma ana yaudarar mutane da cewa anyi sasanci da barayi nikuma Banga wani sasanciba saboda idan suka hadu dakai to lalllai babu wata maganar sasanci kawai kisane ..
Sannan ga jahar katsina abun babu dadin ji ko gani suma abun ya kazanta sosai a koda yaushe garuruwa tashi suke suna komawa su zama mabarata a wani garin Kuma shima wannan kaskancine Amma haryanzu saidai kaji anacewa anyi sasanci wane irin sasanci ahanaka rike makami Amma abokin gabarka Yana dashi..
Lallai talakawa suna cikin wani mawuyacin hali Amma Kuma sunki su farka daga wannann mummunan barci dasukeyi .
Tun farko Allah ya fito Mana da mafita akan wannan abun dayake faruwa Amma anki karbawa Kuma ga wahala halu sunata Kara yawa .
To kusani amsa Kiran sayyed zakzaky shine karshen wannan zalincin saboda shi sayyed zakzaky Yana fada da zalincine Amma sai wasu suka kirashi da Dan fitina kuma Basu San cewa shine gatansuba .
Wallahi gomnati batason talaka ko kadan. To idan mun gano haka mizai Hana mu hadu mu dunkule mu yaki kafircin duniya baki daya Kuma Allah zai tausaya Mana.
To yanzu ga wata ta bullo an Hana hawa mashin da karfe 7::pm shikenan Kuma wannan duka abun wahalar tana komawa ga talakane
Sannan mota an Hana sa mutane a but ko a Dora kaya saman mota to shima idan ka natsu ka duba zakaga duk abunda talaka ya dogara dashi shine basa so ..
Alhamdulllh....................
Allah ka daukaka shafin MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE.
SHAFI MAI FARIN JINI WANDA YA KWARE WAJAN ILMANTAR DA MUTANE DA NISHADANTARWA DA SANIN TECHNOLOGY WATO DUNIYARMU AYAU.
Tags:
Labaran Duniya