Wannan abu da ban tsoro yake!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YA YI KUKA HAR YAKE CEWA, ‘’ ASHE HAKA ZA MU KASANCE A BAYANKA ?‘’

Wannan kadai ya isa zama ishara ga duk wani ma'abucin addini dan gwagwarmaya. Neman tabbatuwa shine babbar addu'ar da ya kamata mutum ya riqa yi a kullum .

Biyewa son zuciya kan sa dugadugan mutum su zame daga kan miqaqqen tafarki ba tare da ya san lokacin ba.

Furucin da Annabi (S.A.W.W )yayi kan Khalifa  Abubakar, da kuma abinda shima ya mayar yayi matuqar firgitani. Wannan dalili yasa naga ya kamata ya kawo shi ga 'yan'uwa abokai don daukar darasi.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Wannan abu ya faru ne bayan waqi'ar Uhud yadda Annabi (S.A.W .W )ya yi kyakkyawar shaida kan wasu, kuma ya qi yiwa wasu don abinda yake tunanin za su iya kasance cikinsa a bayansa.

Ga hadisin nan kamar yadda Imam Malik ya kawo;

An bani labari daga Malik daga baban Nadhri bawan Umar Bn Ubaidullahi cewa labari ya iso masa : Manzon Allah (S.A.W.W )ya fada akan shaheedan Uhud;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ WADANNAN NAYI SHAIDA A AKAN SU (sun gaskata alqawarinsu ga Allah ).‘’

Sai Abubakar Siddiqu yace;

‘’ Ashe muma ba 'yan'uwansu bane yaa Ma'aikin Allah (da ba za kayi shaida a kanmu kamar yadda kayi a kansu ba ), mun muslimta kamar yadda suka muslimta, kuma munyi jihadi kamar yadda suka yi ?‘’

Sai Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

‘’ HAKANE, SAI DAI AI BAN SAN ABINDA ZA KU AIKATA A BAYANA BA .‘’

Sai Abubakar yayi kuka yayi kuka (da jin wannan magana ), sannan yace;

‘’ Ashe haka za mu kasance a bayanka ?‘’

(Muwadda Malik, hadisi na 988)

KITABUL-JIHAD, BABIN SHAHIDAI A HANYAR ALLAH.

Kuma abinda yake jin tsoron faruwar tasa ne ya auku .

YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU KAN GASKIYA .

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        08137925034

~18th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post