Tura takai bango| Yau gaskiya ta fito daga bakin sarkin musulmi!!




MA'ASUMAH HAUSA NIGERIAN NEWS UPDATES

 Tare da Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) Azare

  Zunuban Da Muke Aikatawa Ne Ya Jawo Mana Matsalar Tsaro, Cewar Sarkin Musulmi
Daga Comr Abba Sani Pantami

"Matsalar tsaro dake addabar kasar mu yana daya daga cikin hukuncin da Allah yake mana na kin bin umarnin shi", cewar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III.
Da yake bayani a wajen taron kasa da kasa na biyar da aka gabatar kan “Soyayya da hakuri wajen wanzar da zaman lafiya da kuma rage wuce gona da iri,” wanda aka yi a Abuja.
Sarkin Musulman ya ce ‘yan Najeriya suna zaune cikin aikata zunubai, kuma sunki su bi dokokin da Qur’ani da Bible suka koyar. "Najeriya, ya kawo hadin kai a kasar... "

  *Shine ni kuma nace:- Sarki ya tunasar damu wannan 👇*

  *BABBAN ZUNUBIN DA MUKE AIKATAWA SHINE BIN "CONSTITUTION" BA LITTAFIN ALLAH BA! SHINE BABBAN ZUNUBINMU!, MUCE BAZA A MULKEMU BA SAI DA LITTAFIN ALLAH, ANAN MAFITARMU TAKE DUNIYA DA LAHIRA* Zamu rabu da wannan musibar da muke ciki!.

 Kamar yadda Allah yace:- *"Summa Ja'alnaka ala Shari'atin minal Amri Fattabi'aha wa tattabi Ahawa'allazina Laya'almun"*
 Fassara:- "Sannan mun sanyaka akan shari'a cikin kowane al'amura kabita, (shari'a) kada kabi son zuciyar wa 'yanda basu da Ilimi.
 Kunga kamar "Constitution" ai son zuciyar wasu ne! Toh Allah ya hanamu bin wannan*"

 Mu gyara muna da sauran lokacin gyarawa! Lallai tabbas anan mafitarmu take! Yaku al'umar Musulmi!!!

 Kada muji tsoron kisa ko dauri, mutuna akan addininmu za a kashemu ko kuma a dauremu, kunga kenan bamu da hasara, muna da sakamako mai girma a wajen Allah! In kuma mun mutu! Mutuwar Shahada ce wacce sakamakonta Aljannah ce "direct" kuma ita ce mafificiyar mutuwa.

 In kuma munqi tashi mu gyara, hakan, zamu zauna cikin quncin rayuwa da zillah da wulaqanci da musiba da bala'o'i, da cututtuka iri-iri, kuma bazamu gujewa mutuwar da muke tsoronba zata riskemu cikin wannan Yanayin!

 Maganin haka shine mukoma zuwa ga Allah muce baza a mulkemu ba sai da Littafin Allah bisa turbar Musulunci.

 Zaman lafiya da jin dadi yana ga tsarin musulunci!

 Ku ziyarcemu ta nan don Samun qayatattun labarai masu kuma amfani sabbi, da labaran yau da kullum na cikin gida da waje ta wannan link👇
http://www.maasumah.com.ng

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post