Tunatar dakai, kan al'amarin Jagora (1-6)



@Ma'asumah Nigerian News Update@

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.

Ina jaddada jaje da ta’aziya ga iyalai, iyaye, ‘yan uwa da masoyan Shahidanmu masu girman daraja, tare da rokon Allah ya girmama matsayinsu, ya tsinewa makasansu albarka, ya gaggauta bi mana kadin jinanensu masu tsarki.

Ya ‘yan uwan imani masu girma, hakika masu kokari daga cikinmu sun yi kokari sosai wajen ganin sun ba da kariya ga Jagoranmu, wanda bashi kariya ya kasance difa’i ga Musulunci saboda kasancewarsa babban alamin addini, ma’abocin da’awa zuwa ga Allah da tsayuwa a kan tafarkin Manzonnin Allah.

Masu ba da kariyar nan sun bada ne iyakan iyawarsu, ko da yake wasu sun mallaki hikima, sun sadaukar da shi, wasu sun mallaki arziki, sun sadaukar, wasu kuwa mafi girman mallakinsu rayukansu suka sadaukar a wannan tafarki na tsira da kokarin ba da kariya ga ruhin addini a wannan lokaci, Jagoranmu Sayyid (H).

Idan na tsaya maimaita muku abubuwa, mai sauki ne ya zama mai karatu ya kosa, ko ma ya ajiye karatun, alhali bukata ta shine ya zama an karanta, kuma bayan karantawa din, kila ba za a rasa abu mai amfani a cikin rubutun ba, ko da kuwa kashi 1 ne a cikin 100 (1%) ya zama kowa ya amfanu da shi, ala bashi sauran 99% su kasance ra’ayina, kuma rashin daidai ko dacewarsu zai zama daga gazawata ne.

Ya mu ‘yan uwan imani, da muka amsa kiran mai kira zuwa ga Allah, shin mun jahilci manufa da hadafin Jagoran nan ne, cewa kira ne zuwa ga rusa nizamin da ba na addini ba, da kuma tabbatar da addinin Musulunci a doron kasa? Jagoranmu, duk kuwa da ya ambata cewa babban gudummawar da dan uwa zai ba Harka shine ya gyara kansa, ya fadi hakan saboda da gyaran kan ne ake shiryawa yunkurin kawo gyara a cikin al’umma. Ba yana nufin kiransa kira ne na kokarin tsarkake kai da tarbiyar ruhi kawai ba, kira ne zuwa ga fafutuka, gwagwarmaya, harka ko motsi, don ganin an dawo da addini ya kafu daram a doron kasa.

Wannan hadafi ne na Annabawa da Manzonnin Allah (T) wanda shine dalilin aiko su, kuma a kan wannan ne aka kashe mafi yawansu ba tare da sun rangwantawa dagutu ba. Har kuma aka fassara mana dagutu da ma’anar duk wani abu da ke kishiyantar Allah (T), wanda kuma Kwansitushen din da ke iko da kasar nan, ko jahili ya tabbatar da cewa wani tsari ne da ya yi hannun riga da tsarin Allah (T). Don haka duk mabiyin Annabi na hakika, mabiya tafarkin Annabawan Allah ba za su taba natsuwa da wanzuwar wannan tsarin a cikinsu ba. Wajibi ne su tashi su yi hankoron ganin sun yi kira ga a kyamace shi, har zuwa lokacin da wasu adadi za su amsa kiran, kuma masu rike da tsarin ba za su kyale ba, za su yi ta barazana da aiwatar da ta’addanci, amma a karshe Allah (T) zai dubi ‘yan kadan din da suka dake, ya basu nasara ta inda basu zata ba.

Ya mu ‘yan uwa, na tabbata ba mu manta ba, cewa a kan wannan ne Jagoranmu ya fara kira, a kansa kuma ya dake a kan kira din tun yana shi kadai, har gomomi suka amsa masa, har sadda aka wayi gari yau akwai masu amsa wannan da’awa ta turbar Annabawa miliyoyi a adadi.

Daga farkon al’amari da Jagora yake shi kadai din nan, har suka zama kwarori, sun kasance masu sanin cewa tabbas za su fuskanci jarabawowi da musibu kala-kala, amma saninsu da tarihin Annabawan da suka gabata, cewa sun tashi sun yi kira, wani Annabi bai samu ko mutum 1 da ya amsa masa kiran ba ma aka kashe shi, yasa Jagora suka ji basu damu ba, in ta kama a kashe su ne a kan kiran, akalla sun san cewa za su je wa Allah da irin wannan uzurin na Annabawan da aka kashe su saboda kiran da suke yi, ba tare da an amsa musu ba.

A kan wannan aka kama Jagora, aka rika tsare shi, ya sha dauri kamar kullin goro, muna lissafa cewa an tsare Jagoranmu a wuraren tsarewa fiye da 10, ya shafe fiye da shekaru 12 yana kurkuku a lokuta daban-daban, ya ga jarabawa kala-kala a tsawon shekaru fiye da 40, amma bawan Allah din nan, da yake yana abin da yake yi ne da yakini, kamar yana ganin zahirin alkawarin Allah (T), bai taba gazawa ko ya yi rauni ba.

Har zuwa sadda kafircin duniya ta ga cewa mafita kawai shine ta kawar da shi a doron kasa baki daya, wanda ta yi yunkurin kashe shi da kisan gilla a ranar 12 ga watan Disambar 2015, wanda kafin lokacin nan, sai da aka shekara akalla shida cur! Tun daga 2009 kullum cikin shirye-shirye da kawo masa hari ake da kokarin a ga ya za a yi a kashe shi, amma Allah (T) na bashi kariya.

— Saifullahi M. Kabir
7/2/2020.

TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA (2)

Tsawon shekaru 6 cur, kamar yadda kowannenmu ya sani, tun daga shekarar 2009 lokacin mulkin Umaru Musa Yar Adu’a, hukumomin kasar nan suke ta kokarin sai sun kashe Shaikh Zakzaky. Domin suna ganin kashe shi din ne kawai mafita a gare su, a ganinsu, hakan ne zai kawo karshen Harkar Musuluncin da ke barazana ga nizamin da suke karewa. Haka suma masu ingizasu kan su kashe din, wadanda dama su suka dankara mana nizamin bayan sun rushe nizamin addini da Shehu ya kafa, kullum suna ganin kashe Jagoran ne zai basu damar cigaba da morar abin da suke mora daga nizamin da suka dankara mana din.

Ya ‘yan uwan Imani, Jagoranmu bai boye mana ba, tun a shekarar 2009 din nan yake bayyana mana duk wani kullin azzalumai a kansa da kan da’awarsa, cewa suna nufin su kashe shi ne. A kowane lokaci ba don yana kira zuwa ga mu tashi mu bashi kariya bane, a’a. Jagoran na sanar da mu ne don na farko ya nunawa azzalumai cewa an san abin da suke kullawa, wanda hakan kan sa a wasu lokuta su janye, a wasu lokuta kuma su aiwatar duk da haka.

Har ila yau, Jagora kan nanata mana, don akalla mu da muke ikirarin cewa mu mabiyansa ne, mu Ankara tun da wuri, kar mu yi irin kuskuren da magabatanmu suka yi a tarihi, misalin mutanen Kufa da suka amsa sunan almajiran Amirulmuminin (AS) amma suka gaza bashi kariya har aka kashe shi.

Ah! Baka tambayi kanka cikin mamaki ba, cewa a daren da za a kashe Imam Ali (As) ya yi ta nuna alamun za a kashe shi din, har a masallaci bai buyawa mutane cewa Ibn Muljam na cikin masallacin kuma yana da nufin kashe Imam Ali (AS) ba, amma mutanen da ke masallacin ba su yi tunanin su dauki kowane irin matakin ba da kariya ba har sai da Ibn Muljam din ya daba masa wukar, Amirulmuminin ya kira Allah, sannan suka Ankara suka damke Ibn Muljam?

Kila kace ai Allah Ya riga ya kaddara ba makawa zai auku. Eh! Eh, Allah ya kaddara hakan, ya kuma kaddara cewa hakan zai auku ne a sakamakon sakacin mabiya ga ba Jagoransu kariya. Kana ganin sun kubuta salum-alum ne har a wajen Allah, ba za a zarge su da gazawa wajen baiwa Jagoransu kariya ba har sai da mai aukuwa ta auku a kansa?

Ko ba mu koyi komai ba, a cikin zaman kwanaki 30 da Jagoranmu ke mana duk shekara yana karanta mana Ashura da darussan da ke cikinta? Ban son nace misalinmu zai iya kama da mutanen Kufa, da suka rika aikawa Imam Husaini (AS) wasiku a lokacin da yake Madina da Makkah, a kan cewa zaluncin Yazidu ya ishe su, shine dan Annabi (S), ya zo sun bi shi dari-bisa-dari suna masu mara masa baya, har ya zama wasiku fiye da 30,000 sun riski Imam na amsuwa, wasu da sunan mutum guda, wasu da sunan jam’in mutane. Amma da Imam (AS) ya kamo hanyar Kufa, yana gab da isa rundunar makiya suka tare shi a Karbala da nufin su kashe shi, me ya dace ya kasance?

Wadannan marubuta wasikun fiye da 30,000, ashe ba su cancanci su cika alkawarin da suka wa Imam a yayin da suka gayyace shi ba?  Sai ya zama sun kalli cewa nizamin da ke iko (na gwamnatin Yazidu a lokacin) ya fi karfinsu, saboda barazanar da yake musu da tsoron da aka saka a zukatansu. Aka wayi gari tun da yawansu suna ganin ya kamata kawai su janye daga al’amarin Imam Husaini ne, su zura ido, su masa addu’a, tunda shi dan Annabi ne Allah zai kare shi, har aka wayi wasu rudin duniya ya shige su ma sun amshi bukatar su yake shi. Sai suka juya baya, suka kasance ma’abota butulci da tabewa, a yayin da duk da wasikun mutum fiye da dubu 30,000 na cewa Labbaika Ya Husaini! Aka rasa mutum dari (100) da za su taimaki Imam Husaini din su bashi kariya, har aka kashe shi tare da gomomin da suka sadaukar a gare shi.

Sai bayan da aka kashe Imam Husaini (AS) kuma mutanen Kufa suka koma suna Majalisin Koke-koke a Husainiyoyi da Markazozinsu. Suna cewa Imam Sajjad (AS), mu masu tuba ne a kan sakacinmu na baya, za mu bi ka, za mu taimake ka. Imam ya amshi tubansu (neman yafiyar wanda ya yi nadama ta gaskiya) amma yace wallahi karya kuke yi ya ku mayaudara! Tambaya, sun bi Imam Sajjad din da gaske? Sun taimake shi a bayan hakan har sadda Hisham ya shayar da shi guba ya yi Shahada a lokacin bisa umurnin Walid?

Ya ku ‘yan uwan Imani, lokacin da Haruna Rashid ya kama Imam Musal Kazeem (AS) yasa aka tsare shi, Imam yana da dubban mabiya da magoya baya (Shi’a), amma suka gaza taimakonsa da komai, suna tsoron ta’addancin gwamnatin Haruna. Har daga karshe Haruna ya ga cewa kashe Imam ba zai wani zama masa barazana ba, don haka ya ba gwamnan Basra, Isa Dan Jafar umurni ya kashe shi. Da gwamnan Basra ya nuna yana neman uzuri ba zai iya ba, take Haruna ya sa a dauke Imam daga gidan yarinsa a mai da shi hannun Fadal Al-Rabi, wanda shima Al-Rabi tsabar haibar da ya gani na Imam yasa ya kasa aiwatar da kisa a kansa, Haruna yasa aka mai da Imam kurkukun Fadal Dan Yahya.

Duk kashe Imam Musa (As) ya gagare su, don haka sai Haruna ya sa aka mai da Imam Musal Kazeem (AS) hannun shugaban rundunar sojojinsa a Bagdad, Sindi Dan Shahak wanda shi bai da Imani ko kadan. Karshe Haruna ya aiko Yahya Bin Kalid suka tattauna da Sindi suka saka guba a abinci suka ciyar da Imam Kazeem (AS) a Kurkuku. Suka bar shi sai da ya kwana uku da Shahada, sannan suka fito da gawarsa suka aje a wani waje, suka sa mutane suna cewa, ku zo ku duba ko wannan shine Musa Bin Jafar, gashi ya mutu.

Ance a nan ne Shi’ar Imam Musal Kazeem suka hadu akai ta kuka, bayan da aka hadu a masallacin Juma’a domin masa sallar janaza, wasu na cewa Imam yace za mu ganshi ranar Juma’a, ashe a makara za mu ganshi. Sukai ta tsinewa Haruna suna la’antansa, daga baya suka koma Husainiyyoyi suna zamammakin juyayin Haruna ya kashe Imam Kazeem (AS) a kurkuku.

— Saifullahi M. Kabir
8/2/2020.

TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA (3)

Idan duk abin da muka kawo a baya, na yadda mabiya suka rika yasar da shugabanninsu (Ma’asumai) saboda tsoronsu ga cutarwar azzalumai da irin tsoratasu da suke yi, suka rika gummace su bar Jagoran kawai su bi shi da addu’a, Allah Ya kare shi tunda bawan Allah ne, har sadda za a kashe shi wani zubi a basu gawa a wulakance su yi ta kuka da dana-sanin karya. In duk mun san wannan daga karatuttukan da Jagoranmu ke bamu tsawon shekaru, ‘yan uwan Imani wane darasi muka dauka a cikinsu saboda Allah?

Ashe ba mu zama masu rauni da gazawa ba, a yayin da Jagoranmu Dan Manzon Allah (S), mai kira zuwa ga Allah (T) ya shafe shekaru akalla shida (6) cur yana sanar da mu nufin azzalumai a kansa, amma ba wani mataki da muka dauka a miliyoyinmu da muke tutiyar amsa kiransa, har sadda mai aukuwa ta auku, aka ritsa da shi a gidansa, sojin Buhari kasa da 1,000 suka zo da nufin kashe shi, amma ba a samu mutum dubu uku (3000) daga mabiyansa fiye da miliyan uku da suka zo suka yi kokarin cinye su danyu ba!

Ashe ba karya muke yi ba da muke cewa mu masu bin umurni ne!? Kuna ganin Tarihi ba zai karyata wannan ikirarin nizami da bin umurnin namu ba, idan ya ji cewa a lokacin da aka ritsa da Jagoranmu, wasu manya-manyan almajiransa da muke saurara musu, irin su Shaikh Mukhtar Sahabi, Shaikh Muhammad Turi, Shaikh Mustapha Lawal, Shaikh Qasim Umar da suransu, duk ba kawai sun yi kira ga yan uwa a kai kansu Zariya don ba Jagora kariya bane, a’a, su sun je ne da jikkunansu don ba da kariyar kuma basu gushe ba sai da ya zama basu sannan aka kai ga Jagora. Miliyoyinmu na ‘yan uwa, umurni daga wa suka jira a wannan lokacin kafin su zo su yi kokarin hana Jahiliyya cimma Jagoranmu (H)?

Haris ne kai? Kana jiran Umurni daga kwamandanka Malam Hamza Yawuri ne wanda tun a farkon harin aka shahadantar da shi? Ko kai dan ISMA ne, masu ceton rayukan al’umma? Kana jira ne Dr. Mustapha yace ka zo inda yake ba da agaji ka tallafa masa kafin da bayan an kashe shi? Kai Matashi ne? Dan Dandalin Matasa ko Dan wata Mu’assasa? Kana ina Malam Hafiz Dauda yai shahada? Kana ina ‘ya’yan Jagora suka rika kokarin ba da kariya ana kange su har sai da Shahada ta riske su? Baka ji labarin wasu tsirarun matasa da suka sadaukar ba? Kana ina a sannan? Kai Malami ne a Harka ko me wata mas’uliyya? Su Malam Kabir Alkanawi, Malam Iyal da sauransu duk sun kasance a wajen ba Sharifin Mujaddadi kariya, kana ina a sannan?

‘Yan uwan Imani, idan duk muka tambayi kanmu wadannan tambayoyin, ashe amsar ba zai zama mana cewa lallai mun gaza yin abin da ya dace ba? Musamman idan muka tuna yadda Jagora kan ce, in aka turo jami’an tsaro cikinmu, in duk cikarmu nan aka ce ku kamo su, wallahi wani ba zai samu wanda zai kama ba. In ya fadi hakan mu kan yi Kabbara, mu ce Labbaika! (Mun amsa maka). Wato duk randa hakan ya auku, za mu yanyame su din mu kamo su kenan! Ba mu zama masu saba alkawari ba a yayin da suka zo din muka gaza amsa abin da Mukai alkawari da shi?

In duk mun amince mun yi kuskure, ya ku ‘yan uwan Imani, in mun yarda duk mun gaza a baya har azzalmai sun riga sun cimma Jagoranmu, bai kamata mu yi kokarin ganin mun gyara wannan kuskuren ba tun muna da sauran dama? Shin tsakaninmu da Allah mun gama kure duk abin da za mu yi kenan na fafutukar ganin Jagoranmu ya samu ‘yanci, kuma masu yi masa barazana basu samu natsuwar abin da suke yi wanda kullum yana dada daduwa ne ba?

Me na yi wanda yake tabbatar min cewa har a wajen Allah na kubuta, na sauke hakkin wannan jikan Annabin, mujaddadin addini ma’abocin kira zuwa ga Allah, gatan raunana kuma fansarsu a wajen Allah (T)? Shin nawa nake da shi na dukiya? Kadara nawa na mallaka da na sayar don tallafawa fafutukar ganin an sake shi? Miliyan nawa nake da shi da suka kare karkaf don ya kubuta bai kubutan ba? Dari nawa na sadaukar alhali su kawai nake da su gaba da baya don neman kubutarsa? So nawa na fita Muzaharar kira a sake shi, ina mai yin Allah –wadai da kuma bayyana zaluncinsa?

A kan kokari da fafutukan ganin mutumin da na tabbatar da cewa shine silan tsirana a wajen Allah (T), me ya sami jikina? Gajiya? So nawa aka min rauni? So nawa aka kama ni aka kulle ni kamar yadda yake kulle tsawon shekaru? Me rayuwata ke yi ana cigaba da ta’annuti ga Dan Manzon Allah, Jagorana, har kullum yana fuskantar ajali ne, amma nake kokarin kubutar da raina?

Tsakani da Allah kowannenmu ya tambayi kansa wadannan tambayoyin, ya ba kansa amsa. Cewa shin da gaske ne umurnin wani babba a Harka nake jira don na yi wani motsi don kubutar mafi girma a Harkar baki daya? Ko dai kawai ina cewa ne ba a bani umurni ba, Malam ko Shaikh wane bai ce mu yi kaza ba tukunna, ko shi bai yi ba sai randa na ga ya yi sannan zan yi, saboda hakan ne kawai ya yi daidai da maslahar kaina? In har ba don ina neman abin da ya ma rai da rayuwata dadi bane, da gaske ne don Malam wane bai ce a yi kaza bane yasa bana yi da yace a yi ko ya yi zan yi, ina nake a lokacin da su Malam Turi, Malam Hamza Yawuri, Malam Hafiz, Dakta Mustapha, Malam Kanawi da sauransu duk suka yi wani abu da ni ban yi shi ba?

— Saifullahi M. Kabir
9/2/2020.

TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA (4)

Ya ‘yan uwa masu girma, hakika gaskiya tana da daci matuka, amma Alhamdulillahi da ya zama muna iya gane ta, kuma mu fadawa kawukanmu domin mu tasirantu da ita. Muna rokon Allah (T) Ya sanya mu cikin ma’abota gyara da gasgata nadama.

Ban nufin nace ‘yan uwa ba su sadaukar ba. Ba kuma ina cewa ne ba a yi komai ko ma ba a yin komai din ba. Domin kuwa ko ni da kaina a wasu lokuta na kan zauna na yi ta zanari cewa mene ne ma ‘yan uwa ba su yi ba da ake bukatar a yi yanzu? Kuma da gaske kaina kan kulle na ga kamar an yi komai din, kawai an kure duk abin da za a iya yi ne.

Alhali a hakikanin gaskiya ba haka bane. Na’am, masu sadaukarwa daga cikinmu sun sadaukar iyakar iyawa, wasu sun sha wahala da kishi da yunwa, wasu sun samu raunuka a sassan jiki da suka sabbaba musu jinya, wasu an kama su an tsare su na tsawon lokaci cikin azabtarwar duniya, wasu ma da dama an kashe su ne, sun koma ga Allah cikin jini an kashe su suna Mazlumai Shahidai. Alhamdulillah.

Haka ne. Wasu sun sadaukar da lokacinsu kullum suna fafutuka da kiraye-kiraye tsakanin kotu, hukumomin da ke ikirarin kare hakkin dan Adam, manyan mutane da cikin al’umma baki daya ma. A yayin da wasu suka rika sadaukar da dukiyoyinsu ana daukar dawainiyar masu jinya, daurarru, buga takardu da banoni da belin yan uwa da sauransu. Duk an yi wadannan.

Wasu sun tsayu da Muzaharori a garuruwansu, wasu kuma sun tsayu da yi a Abuja da Kaduna kullu yaumin, safiya da yamma, dare da rana duk suna fita a tsirarunsu suna kira a saki Jagoran Gaskiya. Alhamdulillah.

Tambaya; Kashi nawa ne cikin 100 na ‘yan uwa masu yin wannan din? Tsakaninka da Allah ka kasance cikin masu tsayuwa din da kowane irin nau’in tsayuwa? Yanayinka a sadda Jagora ke gabanka daya ne da yanzu wajen amsa wannan Harkar? In ba haka bane, ya dan uwa mai girma, me ya raunataka yanzu? Waki’a? Yaqini take sakawa ga Muminai ba rauni ba. Me ke samunmu?

In har mun yarda cewa mun gaza a yayin da muka kasa haduwa a cikin miliyoyinmu mu yanyame Zariya a lokacin waki’a, aka rasa mutum 3,000 masu amsa kiran Jagora a sannan, me zai sa yanzu ba za mu yi tuba ingantacciya ta hanyar fitowa a Miliyoyinmu kamar fitan Tattaki da Maulud din nan, muce dukkanmu rayukanmu fansa ne ga Jagoranmu, a sake shi ko duk a kashe mu! ‘Yan uwana, Ko Jagoran namu bai cancanci haka bane?

Idan muka fito kwanmu da kwarkwata muka ce ya isa haka, a sake shi kawai, kana tsammanin zai yiwu ace an wayi gari dukkanmu an kashe mu ne? Da karancin adadinmu a idonmu, ba mu da yakinin Allah (T) zai karawa azzalumai yawan adadin, ya firgita su, ya kawo mana taimakonSa, wala’alla hakan ya zama dalilin maido da hankalin duniya kanmu da kiraye-kirayen da zai zama ba mafita ga azzalumai sai dai su sake Jagoranmu kawai?

Haka ne, na sani cewa azzalumai za su baje iyakan rashin mutuncinsu na kashe rayuka da kai wasu ‘yan uwa kididdigaggu Aljanna. Hakan ne zai kange mu daga sadaukarwa?

Wani na cewa, kana nufin mu yi ta fitowa ana samun Shahidai? Ashe ba a fito Muzaharar Allah-wadai da kisan Shaikh Ahmad Yasin ba, duk da masaniyar za a bude wuta rannan a Kaduna ba a fito an yi ba? Ba a bude wutan ba? Ba a samu Shahidai ba? Shaikh Rantisi ya fi Jagoranmu ne? Ba a fito Muzaharar Qud’s a 2001 an samu Shahidai a Kano ba? Da shekara ta zagayo an saurara ne? Ba mu cigaba da Qudus ba har a 2009 da 2014 aka bude wuta? A 2015 ba a kuma fitowa ba? Qudus ta fi Jagoranmu ne? Ko zaluncin da akewa Palasdinawa ya fi na wanda akewa Jagoranmu ne da muka yarda mu dauwama muna fitowa goyon bayansu ko da akwai barazanar kashe mu, amma muke ganin bai kamata mu wanzu muna fita ana kashe mu kan Jagoranmu ba?

Mu tuna da ‘Method’ din Jagoranmu mana. Dan uwana mai girma, ka tuna yadda Jagora ke fallasa mugun nufin makiya a kansa da kan Harka baki daya? Duk lokacin da azzalumai suka yi mugun kullinsu suna nufin aiwatarwa, Jagora ba ya kan zo ya yi bayani cikin tsoratarwa bane ga ‘yan uwa. Ya kan yi bayani ne ta sigar da su kansu ‘yan uwa za su yi ta kabbara a kan sun gamsu a kashe su a kan wannan abin da su fasa shi. Jagora kan ce mana, yau ma sun shirya za su yi kaza a rana kaza, a lokaci kaza, sun shirya za su yi kisan ba ji ba gani, sun shirya za su saka bama-bamai, sun shirya za su bude wuta, sun shirya za su turo wasu cikinmu su yi kaza. Duk bayan ya kawo shirin, sai ya koma maida musu da martani ta hanyar yin magana da ‘yan uwa cikin yaren gwargwarmaya.

Jagoranmu kan ce, su yi nasu, muma za mu yi namu. Ya kan ce, ba ku isa ku hana mu gudanar da abin da muka fahimta a matsayin addini ba, za mu fito, ko za mu yi kaza, in mutum shine kaza! Ya zo ya shekar da jinane! Ba haka bane ‘yan uwa? A hakan sai kaga yan uwa sun fito sosai, ta yadda abin zai wuce tsammanin azzalumai, dole su janye abin da sukai niyya, ko a wani lokacin su afka din, amma su kare da kunyata.

Kasa da makonni biyu ne aka yi waki’ar ta da Bomb a tattakin yankin Kano, wasu na tambayar ko hakan zai sa a fasa tattakin haka? Shaikh Turi yace ko za su dasa bama-bamai daga nan zuwa Zariya za mu rika takawa muna tafiya, in ta kamata mutum 1 ne a cikinmu zai yi saura da zai shiga Zariya, ba za mu fasa ba. Ba a cigaba da tafiyan ba? ‘yan uwa ba su yi ta cidadowa suna zuwa har sai da aka kara yawa sosai ba? To, me ya rasar da irin wadannan yanayoyin na ruhin sadaukarwa da dakewa a cikinmu a wannan lokacin da aka fi bukatar bayyana yaren gwagwarmaya a furuci da aiki?

— Saifullahi M. Kabir
10/2/2020

TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA (5)

Me ya faru ne, muke ga mun gama yin abin da za mu iya, yanzu addu’a kawai ya rage mu rika haduwa muna yi? Ba mu ji wata ruwaya daga Imam Sadiq (AS) da Jagoranmu ya karanto a yayin Tafsirin Suratul Juma'a ba? Inda Imam (AS) ke cewa: Daga cikin mutanen da Allah bai karbar addu'arsu akwai wanda suke bukatar wani abu, amma suka zauna a gida suna addu'a ba tare da sun fita neman abin ba? Allah ba zai amsa musu ba. Ana addu'a ne, sai a fita neman, sai Allah Ya sa kawo samu a yayin nema.

Me ya faru ne, Mu da muke tsayawa mu taka fareti a gaban Jagora, mu ce masa ‘Da jikinmu, da kudinmu, da jininmu, da ranmu, fansa ne gare ka ya AlZakzaky!’, an wayi gari AlZakzaky na kurkuku daure, mu kuma muna tsoron kar mu fito mu ce bamu yarda ba a kama mu a kai mu kurkukun, ko a kashe mu din a daidai lokacin shi yana fuskantar barazanar kisa ko riskar ajali saboda lalurar jiki?

Dama taron addu’ar na yiwuwa ne kamar da, yanzu ba a kan samu kashi 30 cikin 100 na masu halartar addu’a idan an kira a da ba. Ba a zuwa, shima gangamin addu’ar mun gaji da shi kamar yadda muka gaji da Muzahara kenan? To me ya mana saura yan uwa? Mun cire tsammani, mun bar Allah da Jagoran ne?

Ban son na zargi kowa, amma mu yi hakuri da wannan abin da zan fada, ra'ayina ne, ba kuma lallai ya zama ingantacce ba, cewa da ban mamaki yadda muke tutiya mu matasa ne, wadanda suka samu shiriya a tafarkin gwagwarmaya, amma yanzu muna fifita shirya tarurruka, bukukuwa, da gasa, birbishin tattaruwa kwanmu da kwarkwata muce gwamnati ta sake Jagoranmu ko duk ta kashe mu. Har a makon nan mun ga sanarwar wai wasu Matasa sun yi gasar kwallon kafa, kuma za a cigaba da yi don murnar zagayowar mauludin Imam Ali (S).

Don Allah, idan aka nufi kashe Manzon Allah, a ina Imam Ali ke motsa jininsa? A Exercise? Training? Games? Ko kuwa fita yake ya tunkari makiyi iyakan kafinsa da zimmar a kashe shi ko ya kashe!? Idan misali mu matasa ne yanzu irin Imam Ali a lokacin Annabi, muna cewa muna koyi da shi ne, gasar Muzaharorin kira a saki Jagoranmu ya kamata a shirya a kowace Da'ira a ga su wa suka fi jajircewa, yawan mahalarta, bugawa tare da daga kalolin Posters masu bayyana Mazlumiyar Jagora, kiran gidajen jaridu da sauran abubuwa, ko kuwa gasar kwallon kafa da bukukuwa da sauransu?

Mun koma kamar yanzu hankalinmu tsaf a kwance yake, ba ma tuna Jagoranmu ko mu tashi mu yi Muzaharar kira a sake shi, sai lokacin da aka ce mana yana fuskantar sabuwar barazana ko ciwonsa ya tashi, kai kace ba a cikin barazanar yake kullum ba, kai kace akwai randa ya taba waraka daga ciwo ko barazanar riskar Shahada. Haba ‘yan uwa Muminai?

A yau an wayi gari, kashi 95 na ‘yan uwa mun koma dogaro ne ga kotu. Cewa al’amarin Jagoranmu na kotu ne, kuma mu an riga an haramta mu, don haka fita Muzaharar kira a sake shi musamman a Abuja a yanzu hadari ne tunda mu haramtattu ne, kuma ma Elrufa’I yace ko me za mu yi ba za su saki Malam ba, sai randa kotu tai hukunci, don haka ba wani abin da za mu iya kuma, mun aje komai muna jira kawai a fara lissafin saura kwana uku a koma kotu, an shiga kotu, alkali yace kaza, lauya yace kaza, yanzu an sake dagawa.

Haka ake yi kullum, kaga yan uwa hankali ya tashi ana ta addu’o’i cewa gobe za a shiga kotu da su Malam mu karanta Ya Ladifu kafa 99.9, a yi kaza kafa 33 a tofa, wai hakan da niyyar Allah Ya ba Malam nasara ya kubutar da shi. Sai kuma washe gari a kunna Data ana jiran a ji Alkali yace kotu ta gane Zakzaky bai da laifi, don haka ta ba da odar a sake shi ya tafi gida ya je ya cigaba da gwagwarmayarsa, sai kawai mu yi Salawat mu tashi muyi wanka a shirya a tafi tariya? Haba ‘yan uwa. Mu dawo cikin hayyacinmu mana.

Kotun nan, tun farko Jagora ya fada mana cewa suna nufin su yi kisa ne da sunan kotu. Kisa da sunan kotu imma ya zama a karshen shari’a su ce sun kama da laifi, ko kuma abin da ya fi sauki shine su yi ta jan lokacin shari’ar, a yayin da ciwo ke cin bawan Allah din nan, har a wayi gari Allah ya karbi abinsa. Sun kashe shi da sunan shari’a kenan. Sai ya zama Shahidin Kurkuku kamar Imam Kazim da Imam Al'askari (AS).

Kuma karara muna ganin alamu ai, ba mu ga cewa kullum kara tsufa Malam ke yi ba? Bamu ga cewa kullum jikinsa na kara tabarbarewa bane? Bamu ga cewa kullum ana fama a kan a bar likitocinsa su duba shi ana hanawa bane? Ba mu ga cewa yau shekara kusa biyu kenan, watanni 21 cur da fara kai Shaikh Zakzaky kotun ba, an shiga kotun kusan so 10, amma har yanzu ba a fara ko shari’ar ba, kullum aka je sai a kawo wani banza-hofin abu, shikenan zaman minti 30 sai a ce an daga shari’ar sai nan da kwanaki 60 a dawo?

Ko karantawa Jagora laifukan da ake zarginsa da su fa ba a yi ba za mu ce, tunda an yi bara, an ce bana sai an canza, wanda sai an yi hakan, za a zo a fara shari’a. Shekara nawa za a dauka ana kawo shedu? Ba mu ga sai da aka shafe shekara hudu cur ana kawo shedu kan shari’ar ‘yan uwa na Zariya ba? Tsawon wane lokaci za a dauka lauyoyin Malam na ba da amsa da kare tuhuma da shaidun da aka gabatarwa kotun? Yau kusan wata shida da gama shari’ar yan uwa na Zariya da ake tsare da su, amma har yau wai Alkaliya na rubuta hukunci bata gama ba bare ta yanke, wata nawa za a dauka ana rubuta hukuncin na Jagora da karanta shi bayan an gama? Shekara nawa za a dauka ana shari’ar da suka cancanci mu zura musu ido akan cewa in an gama ta ba za a samu Malam da laifi ba dole a sake shi?

Mu farka ‘yan uwa, mu gane cewa maganar dabban Kaduna na cewa ba tsanani ko takura daga garemu da zai sa ya saki Malam har sai an gama shari’a, ya yi ne don mu karaya mu koma mu ce ai Malam ke da gaskiya a shari’a din, don haka a yi shari'ar har a gama, wanda hakan na basu damar cika burinsu ne.

Ya kamata mu tashi tsaye mu hadu mu yi aiki saboda Allah, mu saka musu ‘preasure’ din da dole su saki Malam ta hanyar janye kara ko fasa shari’ar koma mene ne ma su sake shi kawai ko ba su so. Kuma wallahi muna da ikon hakan matukar za mu nazarci kawukanmu, mu samu haduwa da tsayuwa da dakewa mu tashi mu yi gwagwarmaya da su, wanda a cikin tashi da tsayuwar ne akwai taimakon Allah (T) da agajinSa fiye da zamanmu a yanayin da muke a yanzu.

— Saifullahi M. Kabir
11/2/2020

TUNATAR DA KAI KAN AL’AMARIN JAGORA (6)

Wasu suna cewa me nake nufi da duk dogayen rubutun nan da nake yi? Ina cewa, ina tunatar da mu baki daya ne, cewa Harka Islamiyya tafarki ne na gwagwarmaya da zalunci da azzalumai. Kuma jagoran Harkar nan yana nufin hakan ne a furuci da aikinsa. Don haka ya kamata mu yi wa kanmu tunani mu gane cewa shin mun fahimci abin da ke wuyayenmu kuwa?

Misali, Jagoranmu (H) ya taba cewa: “Inda da gaske ne akwai wasu mutane wai sunansu Boko Haram, sun sace wasu ‘yan mata (na Chibok), da da gaske ne, wallahi da mun kwato su.” Mun tina wannan maganar? Ya Mukai ‘reaction’ a lokacin ma? Kabbara muka kwada ko? Kowannenmu nake tambaya; Shin mun taba zama musamman mun yi nazarin wannan maganar da akai mata rantsuwa? Cewa me Jagora ke nufi? In da gaske din ne su waye za su kwato su din, ta yaya kuma? Ko muna ganin da ace da gaske din ne shikenan Jagora ba ma zai fara fadan hakan bane?

Musamman bangaren samar da tsaro da nizamin Harkar Musulunci, yaushe muka taba yin taron nazarin maganar Jagora ire-iren wadannan, mu fahimci me yake nufi, muka kuma fara shirin samar da yanayin da in na gaske din ya zo za mu cika ‘hope’ din da Jagora ke da shi a kanmu da ya sa yake iya bugan kirji ya yi bayani haka?

Ashe ba mu ji ya fada

Ko da yake gwamnati ke bayan garkuwa da mutane a yanzu, amma da ya zama abin ya ci tura yai Kamari, mun taba zama musamman muka yi nazarin cewa, Jagoranmu (H) ya fadi a Yaumus Shuhada'u 2014 cewa: "Wannan abin da ke fuskantomu a Kasar nan (na kashe-kashe da zaluntar al'umma) ya shafe mu kai tsaye, kuma fuskantarsa da duk irin abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci, kuma duk wanda aka kashe a cikinmu (a kan wannan) Shahidi ne" ba? Mun tuna hakan? In ba Jagoranmu shikenan komai ya daidaice kenan sai dai mu rika cewa Amawa, duk abin da ke faruwa sakamakon taba Jagoranmu ne, Allah ya kara? Shine alkiblar Gwagwarmayar Musulunci kan lamarin? Wane abu muka yi na kokarin cika zancen Jagoran al'umma (H)?

Abin da nake cewa shine, su mutanen nan sun kama Jagoranmu ne sun kulle bayan da suka nufi kashe shi Allah ya raya shi, saboda su kautar da mu daga hadafin Jagora din na kokarin samar da yanayin da zai yi Muqawama, ya yi gwagwarmaya, ko fada da zaluncin nizamin zalunci a kasar nan. Sai suke ganin a sadda suka kama shi, shikenan za mu gaji har mu koma kawai muna yin taruka irin yadda ‘yan Shi’ar kasuwa ke yi, muna cewa Yazidu tsinanne, muna cewa ana zalunci amma saboda an taba mu ne ake yin zaluncin ma, sai ya zama wadanda muke kira Amawa sun dena fahimtarmu, sun cire fata daga gare mu, bare ai batun wai wata rana za mu yunkura mu kwata musu yanci su mara mana baya.

Mafitarmu kwara daya ce, ita ce gwagwarmaya a tafarkin Allah, wanda kai tsaye shine tashi a yi duk wani abu da zai dakile azzalumi daga zaluncinsa a kan Jagora da kan al’umma baki daya, wanda in da ace sun ga cewa ko ba Jagora ba zai yiwu su mike kafa su yi zalunci yadda suke so ba, za mu taka musu burki kamar shi, da za su ga ba su da bukatar kawar da shi kadai, ko cigaba da tsare shi. Amma in aka wayi gari suka ji muryarsa ce kawai da ta wanzu ke fada da zalunci, aikinsa ne kawai sadda yake waje ke nuna cewa Harkar Musulunci motsi ne na neman yanci da kawar da zalunci da shimfida adalci, to tabbas za su gane sun yi galaba, kuma ba za su sassauto ba. Za ma su ga cewa kawar da shi ne kadai mafitarsu.

A yayin da nake karkare wannan rubutun nawa, ina mai kira garemu baki daya, da mu zauna mu yi nazari manya da kanananmu, kar mu ce kanmu ya kulle mun rasa abin yi, abin yi kwara daya ne, shine fitowa kwanmu da kwarkwata a ko da yaushe ba tare da mun nuna gazawa ko gajiyawa ba, muna masu kira a saki Jagoranmu. Idan har mai zalunci bai saurara na kwana daya ba, wanda ake zalunta ko mai kokarin kawar da zalunci bai ga ta hutu ba.

Ya wajabta ga ‘yan uwan da Allah Ya hore musu miliyoyi da dubban daruruwan kudade suke juyawa, suke sayan gidaje da filaye da kayayyaki, suke kara aurarraki da dinka sabbin shaddoji da yi wa wadanda suka ga dama kyaututtukan bajinta, su gane cewa dukiyar Allah Ya ara musu ne don su yi aiki wa addininSa, kuma a cikin hidimtawa addinin ne albarkar Dukiyarsu duniya da lahira yake, a cikin yi masa rowa ko tsakura masa wani abu cikin dacin rai ko cikin neman yabo ba kawai akwai asara ne ga dukiyar ba, akwai saraya da tabewa ne a gare su.

Ahlud-Dusur (Yan kasuwa da Manoma), Resoureces Forum (Ma’aikata), da sauran ‘yan uwa baki daya na Harkar Musulunci mu wa Allah mu samar da yanayin da zai zama mun kawar da tsoron wasu abubuwan da kudi ke yi wajen fafutukar kiran a saki Jagoranmu wanda shine dalilin shiriya kuma silan tsirarmu a wajen Allah (T).

Abin kunya ne sosai ya zama akwai masu gina gidajen miliyoyin kudi, suna da kantina da masana’antu da shaguna suna juya kudi, amma ai waki’a a ji wa ‘yan uwa 10 rauni ace an gaza samun mai ba da Miliyan daya a kula da maganinsu har sai sun galabaita ana neman tallafi kana bada naira dubu 20 ko 50. Ba ka fahimci cewa kai Harkar naka na iya zama ba da wannan infakin bane, wasu su wakilce ka a ba da lokaci, jiki da rai kamar yadda ka wakilce su a dukiya? Kar aji ina ta maganar masu miliyoyi, shi mai Infaki mai Infaki ne ko da Naira daruruwa yake da shi. Kuma Allah Ya san kowa.

Ya ‘yan uwa masu girma, mu dena bawa kanmu uzirori, Muzaharori za mu tsayu da su kamar yadda muka faro a farkon waki’a da yawanmu na adadi da ruhin Imani da Kankan da kai ga Allah (T) har ya zama mun samar da yanayin da al’amarinmu zai zama labaran duniya, wannan hanyar ya fi komai saukin kusanta mu da nasarar Allah (T).

Al’amarin Muzaharar Abuja da ta Kaduna, abu ne da ya fi kowane abu muhimmanci mu karfafe shi, in aka wayi gari dukkanmu mun fahimci cewa da motsi ne makiya za su gane cewa ba su yi galaba a kanmu ba, to ya kamata duk mu kasance tare da masu motsin a aikace da gangunan jikkunanmu gwargwadon hali, da kuma dukiyarmu musamman ga wanda har a wajen Allah ya tabbatar cewa yana da uzurin da ba zai iya kai samuwarsa wajen Muzaharar ba.

Mu yi abin da har a gaban Allah (T) za mu iya tsayawa mu da Shi, muce masa Ya Ubangijinmu, mun tashi mun tsaya kyam don kokarin adalci ya tabbata kan al’amarin bawanKa, duk da makiya basu gushe ba suna zaluntarmu, ba mu gushe ba muma har sai da muka samu nasarar cimma manufar tsayuwar tamu, ta hanyar kubutarsa ko ta hanyar riskar kyakkyawar rabo (Shahada). Namu mu sauke wazifar da ke kanmu, Natija kuma na wajen Allah (T) ne.

Ina neman yafiyar duk wanda na bata masa rai. Ina kuma rokon afuwar duk wanda bai fahimceni a wata gaɓa ba. Kamar yadda nace, tunatarwa ce kawai, in aka samu kashi 1 cikin 100 na daidai a cikinta, ina fatan mu hadu mu yi aiki da ita. Allah Ya ji tausayinmu, ya bamu ikon tsayuwa a tafarkinSa.

— Saifullahi M. Kabir
11/2/2020.

Compiled—Ansar mashi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post