Tuna Baya GARGADI GA WADANDA SUKE CIKIN GIDA SUKE TAIMAKAWA MAKIYA.

To gargadi ga wadanda suke cikin gida wanda suke taimakawa Makiya; duk wani wanda yake da’awa na raba kawukan Musulmi, wallahi summa tallahi, kuma Billahil lazi la’ilaha illahuwa Karen Yahudu ne! Duk wani wanda ka gani yana kokarin ya fidda da wani Musulmi daga Musulunci, wallahi su yake yiwa aiki! Ba Musulunci yake yiwa aiki ba.

Saboda haka karka zama ma’aikacin su kana cikin Musulunci. Idan yadda Manzon Allah ya iya zama da kowane irin mutum, haka nan Musulunci ya koyar da mu. Kasarmu nan ko mun ki ko mun so haka nan zamu zauna yadda muke din. Zama ne ya hada mu, da kyakkyawan dabi’unmu ne zai nuna ma sauran mutane meye addinin nan, kuma alhamdu lillahi suna ganewa. Yanzu jama’a yanzu wannan yake damunsu hatta a kasashen Turawa din, suna ganin yadda mutane suke binciken Musulunci suke ganewa. Shi ne abin ya dame su suke ta kokarin su yi fada da shi. To, wannan shi ne kaka-tsara-kakan da aka yi mana.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Yanzu kowannenmu ya yi kokarin ya fahimci mene ne addinin nan? Ya aikata, wane ne Annabin nan, ya yi koyi da shi. To, wannan ne ainihin zai turmutsa hancin Makiya, kuma insha Allahul Azim ko an ki ko an so sai addinin nan ya dawo ya kafu Daram!

Su ko makiya Allah ya daidaita al’amarin su. Wannan Ebele Jonathan din nan, Allah ya tsine masa, bashi kadai bama, duk mai goyon bayansa Allah ya tsine masa. Wanda ya ji haushin na fadi haka ma, Allah ya tsine masa.

Inji Shehu Zakzaky a Maulidin Manzon Allah na Khatma a garin Zariya.

Auwal Yusuf Muhammad
Ma'asumah Najeria news Updates
#18/2/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post