Tambaya: Shin, da gaske littafin Allah da Sunnar Annabi (s.a.w.w.) aka bar mana???
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
An sami sabani cikin musulmi wajen sani haqiqanin abubuwan da Annabi (S.A.W.W )ya barwa al'ummarsa a matsayin abin riqo bayansa don kada su halaka.
Wadanda aka fi sani da mabiya mazhabar Ahlul-Bait (A.S )('YAN SHI'AH )sun tafi kan cewa Annabi (S.A.W.W )ya bar littafin Allah ne da iyalan gidansa (A.S )a matsayin abin koyi cikin addinin muslimci . Wanda hakan ya zama daya (1)daga cikin hujjojinsu na yin riqo da Sayyidinah Aliyu a matsayin khalifan farko.
Sai dai kuma wasu bangaren sun tafi ne kan cewa lalle littafin Allah da sunnar Annabi (S.A.W.W )aka bari wacce suke cewa ‘’ KITABU WAS-SUNNAH ‘’. Sune wadanda ke cewa Sayyidinah Abubakar ne khalifan farko bayan Manzon Allah (S.A.W.W
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
).Masu wannan fahinta ko ra'ayi sun dogara ne da wani hadisi da yazo cikin Muwadda-Malik inda yake cewa:
An bani labari daga Malik cewa (labari )ya iso masa;lalle Manzon Allah (S.A.W.W )yace:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ NA BAR ABUBUWA BIYU A CIKINKU WADANDA BA ZA KU BATA BA MATUQAR KUN YI RIQO DA SU . LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI .‘’
(Hadisi me lamba 1614).
Sai dai kuma khalifa Umar Bn Khaddab bai yarda littafin Allah da sunnar Annabi (S.A.W.W )su kasance jagorori gare shi ba, domin ya ce shi littafin Allah kadai ma ya ishe su ba tare da sunnar Annabi (S.A.W.W )ba.
(Bukhari , hadisi na 7366).
To, idan ka auna maganar khalifa Umar da hadisin Imam Malik, wanne irin hukunci za ka fitar?
Za ka qaryata hadisin Kitabu was-Sunnan ne?
Ko kuma cewa za kayi Umar ya yi watsi da wasiyyar Annabi (S.A.W.W )?
Ko kuma dai yana qaryata hadisin ne ?
KU TAYA NI NAZARI DAI !
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~16th February, 2020.
Tags:
Taskar ilimi