Takaitaccen Tarihin Shahid Ishaq Muh`d



Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 Updates
Shafi Domin kai Da Al`Ummar ka


An haifi shahid ishak a garin birnin tudu shiyar zaki gidan bugaje Dake Cikin mafara Local Govt A Jihar Zamfara,  ya rasu yana da Shekaru 27 aduniya.

Yayi primary à modal primary school nan Birnin Tudu Daga 1998 zuwa 2003 daga nan yashiga makarantar secondary a Anka GOVT science school daga 2004 zuwa 2009 yakare,

Daga nan yaje Lagos a navytown secondary school Lagos Amman shahid Allah bi kaddara yayiba saboda shi ya kare secondry kuma yaje can ashe wata secondry ce zai kara sai shahid bai tsaya ba.
To daga nan shahid ya dawo sokota daga 2011_2012 inda ya hadu da mai gida tun kusan shekara takwas suna tare Amma ta bakinsa bai taba cutardashiba.
Lokacin da AKAI mai jana'iza ake ce masa su suke tare da ishak ko sunsan da wani wannan yake bin sa bashi sai yake cewa shi baya cin bashi duk nanurar da zata sashi cin bashi shi hakuri yake da ita sai dai shi yabika shahid kenan.

SHAHID ISHAK MUH'D SULEMAN LOKACIN YARINTARSA


Kaman yanda na zanta da mahaifiyar shi shahid Ishaq akan  take ceman shi shahid ba komai acikin sa sai barkwanci da wasa da dariya,
Take ceman shi yakasance a duk lokacin da ya lura Randunan su ba Ruwa A gida zai rika dibar ruwan har sai ance ya bari,  shi kuma  yace sai ya cika komai a shiyar.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Kuma take ceman wata rana makwabcinsu ya aza wakensa sama sai tsuntsu yadami waken da batawa ,   sai shi shaheed ya aza alamar dazatasa shi tsuntsun yaji tsoro yadaina hawa,  sai shi shahid yadauki abun wani alami na ban dariya haka dai yataso da Abubuwa na barkonci...

Sai muke ce mata koshi  shahid Yataba yi mata wani abu


Sai take cewa shi shahid bai taba mata laifi ba haka ma mahifinsa yake cewa shi bai taba mai laifi ba.

Sai muke tambayarsu ya suka ji labarin shahadar  sa sai mahaifiyar take cewa

lokacin da mal baban gida da yasansa Ahmad zai fada mata sai take cewa aiba sai anfada mata ba saboda ita ta san komai. Haka ma mahaifinsa yake cewa akullun yana  samun sallar asuba amma a wannan rana bai samu ba sai ku san asuba lokacin baci mai nauyi yazo masa,  Tun lokacin Naji cewa akwai wani Abu dazai faru da Shaheed..

ISHAK MUH'D SULEMAN LOKACIN JINYA


An harbi shahid a ranar jumu,a ranar 27/12/2019

Yayi jinyarsa ta sati biyu ne.
Lokacin da aka harbi shahid ninaje Sokoto ranar Assabar da safe nida mal Anas faru muka zo dashi.

Lokacin da shahid yaji wannan raunin bai daukai wani abu ba,  amma duk lokacin da wani yazo zaiganshi sai ace ya shahidi mai rai kun samu naku rabo muma Allah bamu irintaku sai yace: - eh Amman babban rabon nanan zuwa insha Allah.

Shahid yayi wannan satin ne hannun baya damunsa sai kacema ba`a harsbeshi ba,    wata Ranar Jumu`a cikin Sati na biyu da mashi Raunin dakansa yaje mafara yayyi Sallar jumu,a dashi da anas tun daga can yace amai annuran ciwon Dayan hannun don yaji yana masa radadi da zugi ashe tatanus ce ta shiga ga ciwon,

Daga wannan daren har safe shahid hannunsa  nadamunsa  saboda Haka sai ya kirani inzo namasa annura nace yaci abinci yace hannun sa bai kaiwa zuwa bakinsa daga nan muka fara tunanin tatanus ce ta kama shi  ankayi mai diclofenac da ceftriaxon anka hada mai da iv ringerslactate daga nan ciwon sai tsanani yake karawa. YA ALLAH..



Daga nan muka wuce mafara wajen isma suka ce muje asibiti mukaje tare dasu ankayi mai abundai za,ai mai tun ranar Assabar har ranar Laraba shahid bai ce komai amma maganan da take Futa daga bakinsa Kowa ya jiya itace Kalmar dayake Karewa wato la,ilaha,illah wannan wallahi haka take dani da anas da Ahmad da muzanbilu da dady Bello wadannan duk sun shaida haka.

Haka muka ta jinyar shahid har aka kai ranar Laraba babu sauki sai akai mana referral zuwa usman danfodio teaching hospital mukaje daga Wednesday har zuwa Friday har take shahid bai cewa komai saboda annuran da ake masa na bacci Saboda ciwon yana bukatan barci har take baba bai cewa komai daga nan har zuwa jumu,a shahid baice komai ba.

SANADIYAR HARBIN SHAHEED HAR ZUWA SHAHADAR SA


      _=Kamar yadda muka sani yan uwa almajiran sayyid zakzaky h suna gudanar da muzaharori a tsawon Shekaru kusan biyar domin Neman yancin jagora Wanda azzalumai fasikan shuwagabanni Nigeria suke rike dashi bayan abun da ya faru na kisan musulmi almajiran sayyid zakzaky h da rusa gine gine da nufin kashe jagora dama kawarda  harkar Baki daya to wannan ne yasa yan uwa suke fita duk bayan lokata domin Neman yancin jagoran,.

    _A ranar jumu'a 27 ga watan disamba yan uwa na garin sakkwato da sauran sassan kasar nan suka fito suna rera take  suna bayyana bakin cikinsu na rike jagoran su sayyid zakzaky h Wanda azzalumai suke tsare dashi tsawon shekara hudu ba tare da ka'ida ba.

    To a wannan ranar jumu'ar anyi muzaharori ko'ina lafiya amma a sokoto azzalumai na garin sokoto bari aka kammala lafiya ba bayan anyi muzahara anzo gun da za'ayi addu'a sai jamian tsaro da mugun nufinsu suka dinga ruwan tiyagas amma sai ya zamto tiyagas din suna harbashi amma yana dawo masu sakamakon iskan da ake yi to da suka ga haka sai suka fara harba harsasai masu rai inda suka raunata yan uwa da dama sannan suka shahadantar da mutum daya nan take ba tare da bata lokaci ba to shi Dan uwa Ishaq Muhammad yana daga cikin wadanda aka jikatta a hannun hagu a yatsansa mai bima karami yatsan to dalilin haka ne ta jawo aka yanke yatsan nashi aka yimai dressing a hannun sannan a ranar asabar ya dawo gida birnin tudu domin hankalin uwayensa ya  kwanta a wannan halin ya zauna gida tsawon sati daya yana jinyar hannun nasa ana wankeshi yana kuma zuwa mafara a gun wani likita ana yimai dressing sannan yana amfani da magunguna domin kashe zafin ciwon har tsawon wannan satin.

  To a ranar jumu'ar data zagoyo ne hannunsa na dama ya fara ciwo yana masa zugi a wannan ranar bai zauna cikin jin dadi ba har ya kwanta Daren asabar to wayen garin asabar ne Allah ya kaddara masa  da ciwon wuya Wanda bai iya juya shi koina to ni a wannan ranar ganin cewa shi zai kwanta dakin da make kwana gashi dakin karami ne ba girma ne dashi ba sai naje dakin wani abokina na kwanta to koda safiya tayi sai na cimma wuyansa yana mai ciwo had takai ga baya iya komai da wuyan domin an rikeshi kam sannan hannun nasa baikomai harma a gabana ya aika aka karbo mai abinci gurin babarshi domin yaci amma ina kallonsa yayinda ya dauko l
Cibi yakai bakinsa sai ya Gaza kaita baki ya mayar ashe abincinda zaici  kenan  a duniya sun kare sai muka daukeshi mukaje mafara bayan duk anyimasa abun da yakamata ayimai da gaggawa to da muka kira wani daga cikin yan isma Wanda kuma shine kemai dressing a hannun da aka harba sai yace my cimmasu markas da muka he gurin su sai suka ce muje asibiti ganin halin ya tsananta masa

Shahadar Ishaq Muhammad Suleman wani babban al'amarine Wanda ya zamo abun alfahari Wanda ya kawo wani iron chanji da kuma wata


Sai ranar shahadarshi da yake ambatar kalmar shahada a bakinsa..


RAYUWAR SHAHID ISHAK MUH'D SULEMAN AFAGEN BADA TAIMAKO DA SALLAMAWA AL,AMARIN JAGORA..,,,,,,,
,, _


Shahid yakasance mai   kokari da Sallamawa al,amarin Jagora kamar Yanda kanin Babansa yake cewa in ya dawo daga Sokoto aka ce mai Mafara Ana Muzahara to in dai baiyo nisa ne ba to zai wuce mafaran ne in kuma yazo gida jakar sa kawai zai aje ya wuce wajen muzaharar.

Shahid agarinsu shi yake fara biyan kudin shuhada,U  ta Inji kanin Mahaifinsa wanda shine yake karbar kudin, sannan ko wani infaki ne dazaran an kira shi ana gayamar da kyar yayi kwana biyu bai bada ba.

Sadauki ne jarumi Dan Media Wanda yana Daya Daga cikin Wakilan Shafin ma`asumah nigeria 🇳🇬 news 📰  Updates  damu bamu sani ba sai Bayan Shahadarsa , domin inajin wajen kyamarin ne na  Aikinsa da yake aka harbi wayar shi har aka kire yatsan nashi,  tare da sanadiyar shahadar sa,. Tabbas shaheed jarumi ne na gaske.

Shahid yakasance baya karya baya cin Haram yana da tsantseni sosai acikin lamarunsa.

Shahid awajen sada zumunci wannan shine babbar halayyarsa duk sanda ya dawo gida farko abunda yake yi shine sada zumunta uwaye yan uwa da abokan arzuki.

Shahid baya karya baya karya alkawari a iya sanina da shahid tun ina ƙarami muka taso bantaba ganin yayi karya ko saba alkawari ba.
Ba abunda nasani garai sai mukarimul ahlaq inji Abokinsa


Amincin allah Yatabbata gareka ya shahid

ABUBUWAN DA SUKE BADA MAMAKI DANGANE DA AL,AMARIN SHI SHAHID.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


  Daga cikin abubuwan da suka bani mamaki da alajabi akan shahadar Dan uwa Ishaq Muhammad shine a lokacin da ya dawo gida ya gayaman cewa shi wannan abun daya sameshi ba bisa hadari bane domin a Daren jumu'ar da abun ya faru yayi mafarki an harbeshi a hannun to da ranar jumu'a sai aka yi muzahara to amma a lokacin da aka fara sai ya kama dubawa ko'ina ko zaiga jami'an tsaro amma bai gansu ba sai yace shi yayi mamaki baiga mutanen nan ba to sai aka cigaba har akazo wajen rufe muzaharar to lokacin da ya gansu kawai sai yace yanzu kam ya gamsu.

To lokacin ruwan wutan ne suka harbesa a hannun.

Jana'izar malam Ishaq Muhammad ta isar da sako kala kala Inda mutanen garin birnin tudu suka dinga tattaunawa a wuraren da al'umma suke zama dangane da al'amarin takai har wasu suna cewa shin shi wannan wane irin mutum ne ganin irin yadda mutane daban daban wurare daban daban sukayi cincirindo domin rakiyar wannan shahidi kai ma  abun da ya bawa mutanen mamaki shine ganin yadda mutane suka je da mashina suka je har wani guri da ake cima ocha kafin kaje garin birninin tudu domin tarbon gawarsa bayan anzo da gawarsa daga sokoto, wannan ya ba mutane mamaki kwarai.

Gaskiya wannan abun ya dada darajar birnin tudu sosai domin a tsawon garin ba'a taba samun taro irin wannan ba Wanda ya Tara al'umma masu tarin yawa to wallahi ni wannan ya kara man kwarin guiwa sosai ganin wannan daukaka da ta bayyana garemu kuma muna jaddada bai'armu ga jagoranmu sayyid zakzaky h sannan muna tawassuli da Jinan nan wannan bawa naka Allah ya   azurta da  shahada sai a yau dinnan ma wasu mutane daga cikin masu aikin kamfani Wanda yake yin wani aiki a garinmu suke tambaya cewa wannan wane irin mutum ne koko wani babban ma'aikaci ne ko wani babban malami ne.


sannan a yayin da aka je makarbata wajen ziyara bayan an kammala jawabai daban daban dangane da rayuwar wannan shahidi akwai wani chanis daga cikin yan chanan da suke da mallakar kamfanin lokacin da aka bi hanya domin zuwa makarbata sai yaga mutane dauke da hotunan wannan shahidi sai abun ya bashi sha'awa sai ya sauke glass din mota ya Ciro wayarshi ya kama daukar hoton shahidin.

Tabbas Shaheedi kazamo abun girmamawa da kowa , illahy ya kara ainci agareka tun daga ranar haihuwarka har zuwa ranar Shahadar ka da ranar da zaku tashi kuna a shaheedai.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post